Trends

Farashin Fetur Ya Tashi da Kashi 643% Tun Bayan Cire Tallafi

Farashin man fetur (PMS) a Najeriya ya tashi daga Naira 175 kan kowace lita a watan Mayun 2023 zuwa Naira 1,300 a watan Mayun 2026, wanda ke nuna ƙarin kashi 643 cikin 100 cikin shekaru uku da suka gabata.

Wannan hauhawar farashin ta biyo bayan matakin da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na cire tallafin man fetur nan da nan bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, lamarin da ya sa farashin fetur ya haura Naira 500 kan kowace lita.

Daga bisani, faɗuwar darajar naira ta ƙara ta’azzara lamarin, inda ta sa shigo da fetur daga ƙasashen waje ya zama mai tsada ga yawancin ‘yan Najeriya.

A tsakiyar shekarar 2023, Nigerian National Petroleum Company Limited ta fara abin da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya kira “ɓoyayyen tallafi”, inda ake sayar da fetur ƙasa da farashin saukarsa ƙasar nan.

Tsohon Babban Jami’in Kuɗi na NNPC, Umar Ajiya, ya taɓa bayyana cewa suna shigo da fetur ne da wani farashi, amma gwamnati ta umurce su da su sayar da shi a kusan rabin wannan farashin, inda bambancin ya zama asara.

Farashin fetur ya kai Naira 1,080 kan kowace lita a shekarar 2024, daidai lokacin da Dangote Refinery ta fara aiki, wanda ya haifar da gasa a kasuwa tare da saukar da farashin zuwa tsakanin Naira 800 da Naira 900 na ɗan lokaci.

Sai dai rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran a watan Fabrairun 2026 ya kawo cikas ga samar da mai a kasuwannin duniya ta mashigar ruwa ta Hormuz, lamarin da ya sake ɗaga farashin fetur zuwa tsakanin Naira 1,300 da Naira 1,400 a gidajen mai.

Hauhawar farashin ta ƙara matsin tattalin arziki, ta jawo tashin kuɗin sufuri da kuma ƙarin farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.

A matsayin mafita, Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Shirin Shugaban Ƙasa na Amfani da Iskar Gas Mai Matsewa (CNG), amma har yanzu ba a samu karɓuwa sosai ba.

Masanin tattalin arzikin makamashi, Adeola Adenikinju, ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta tallafa wa gidaje masu rauni da kuɗi kai tsaye, yana mai gargadin cewa tsadar fetur na kawo ƙarin kuɗaɗen shiga ga gwamnati amma kuma yana ƙara jefa jama’a cikin wahala.

Shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya yi gargadin cewa farashin fetur na iya haura Naira 1,500 kan kowace lita idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

Shi ma masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, ya ba da shawarar a sayar wa Dangote Refinery ɗanyen mai a farashi mai sauƙi domin daidaita farashin fetur a kasuwa.

Sai dai Ministan Kuɗi ya yi watsi da yiwuwar dawo da tallafi ko sanya dokar sarrafa farashi, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da barin kasuwa ta ƙayyade farashin kayayyaki.

Labari: Punch