Trends

Harkokin Kuɗi: CBN Ta Kaddamar da Tsarin Cimma Kashi 95% na Shigar Jama’a

Yemi Cardoso Shugaban babban Bankin Najeriya wato CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaddamar da Nigeria Payment System Vision (PSV) 2028, wani sabon tsari da ke da nufin kaiwa ga kashi 95 cikin 100 na shigar ‘yan Najeriya cikin harkokin kuɗi nan da shekarar 2028, tare da bunƙasa biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani da kuma mayar da Najeriya cibiyar hada-hadar kuɗi mafi girma a Afirka.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin a Abuja, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana PSV 2028 a matsayin wani tsari da zai sauya yadda ‘yan Najeriya ke gudanar da mu’amaloli, adanawa, zuba jari da kuma shiga cikin tattalin arzikin zamani.

Cardoso ya ce, “A yau, ba kawai muna ƙaddamar da dabarar biyan kuɗi ba ne, muna ƙaddamar da hangen nesa kan yadda ‘yan Najeriya za su yi ciniki, kasuwanci, adanawa, zuba jari da shiga cikin tattalin arzikin da ke ƙara dogaro da fasahar zamani.”

Ya bayyana cewa wannan shiri na iya kawo ƙarin mutane miliyan 50 cikin tsarin kuɗi na hukuma a faɗin ƙasar.

Sabon tsarin ya ginu ne kan nasarorin da Najeriya ta samu a fannin fasahar kuɗi (fintech) da kuma canja wurin kuɗi cikin sauri, inda ake sa ran zai rage dogaro da kuɗin hannu, ƙarfafa cibiyoyin biyan kuɗi da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki.

Daga cikin manufofin da aka sanya a gaba akwai rage yawan kuɗin da ke wajen tsarin banki zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100, samar da wuraren karɓar biyan kuɗi ta QR Code da fasahar “tap-to-pay” sama da miliyan 10, da kuma rage asarar da ake samu ta hanyar damfara zuwa ƙasa da kashi 0.001 cikin 100 na dukkan mu’amaloli ta hanyar amfani da fasahar basirar wucin gadi (AI) da ingantattun hanyoyin tantance bayanan masu amfani.

Cardoso ya kuma bayyana cewa tsarin biyan kuɗi na Nigeria Inter-Bank Settlement System (NIBSS) na sarrafa miliyoyin mu’amaloli a kullum, inda mafi yawansu ke kammala cikin ƙasa da daƙiƙa 10, tare da shirye-shiryen ƙara inganta sauri da amincin tsarin.

Har ila yau, tsarin PSV 2028 ya ba da muhimmanci ga tsarin Open Banking, inda sama da APIs 100 masu lasisi ke tallafa wa kirkire-kirkire da sabbin ayyuka a fannin kuɗi. Haka kuma, shirin na da nufin amfani da damar da ke cikin African Continental Free Trade Area domin sauƙaƙa hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen Afirka.

Ana sa ran wannan shiri zai faɗaɗa damar samun ayyukan kuɗi na zamani ga mata, manoma, ‘yan kasuwa da matasa masu sana’o’i, tare da dacewa da manufofin gwamnatin Najeriya na ƙara yawan aiki da kuma jawo hankalin masu zuba jari.