Trends

Babu Shaidar Cutar Hantavirus a Najeriya – NCDC

Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, Nigeria Centre for Disease Control and Prevention (NCDC), ta tabbatar da cewa babu wata shaida da ke nuna bullar cutar hantavirus a Najeriya, duk da rahotannin da ake yadawa a duniya game da barkewar cutar da aka danganta da wani jirgin ruwa na yawon bude ido.

A cikin wata sanarwar lafiyar jama’a da hukumar ta fitar ranar 8 ga Mayu, NCDC ta bayyana cewa tana ci gaba da sanya ido sosai kan sabbin cututtuka masu yaduwa tare da bibiyar duk wani sabon ci gaba da ke faruwa.

Sanarwar ta biyo bayan damuwar da wasu mutane suka nuna a shafukan sada zumunta cewa barkewar cutar na iya zama kamar yadda annobar COVID-19 ko cutar Lassa fever ta yadu a baya.

NCDC ta jaddada cewa cutar hantavirus galibi tana yaduwa ne ta hanyar cudanya da beraye masu dauke da cutar, fitsarinsu, kashinsu ko yawunsu.

Hukumar ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da su tabbatar da tsaftar muhalli, su rika adana abinci yadda ya kamata, su zubar da shara cikin tsari mai kyau, tare da amfani da kayan kariya yayin tsaftace wuraren da beraye suka mamaye.

“Hukumar NCDC za ta ci gaba da kare lafiyar jama’a tare da bayar da sahihan bayanai a kan lokaci yayin da ake bibiyar halin da ake ciki,” in ji sanarwar.

A matakin duniya kuwa, World Health Organization (WHO) ta bayyana cewa an samu mutane bakwai da ake zargin sun kamu da hantavirus a wani jirgin ruwa na yawon bude ido tsakanin ranar 6 zuwa 28 ga Afrilu.

Rahoton WHO ya nuna cewa mutane biyu sun kamu da cutar a hukumance, biyar ana zarginsu da kamuwa, yayin da mutane uku suka mutu.

Alamomin cutar na iya bayyana tsakanin mako guda zuwa takwas bayan kamuwa da ita, inda ake fara ganin zazzaɓi, gajiya, ciwon kai da ciwon ciki, sannan a wasu lokuta masu tsanani cutar kan kai ga matsalar numfashi ko lalacewar koda.

WHO ta kuma bayyana cewa yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum abu ne mai matukar wuya, sai dai an taba samun wasu ‘yan kalilan da aka danganta da kwayar cutar Andes a nahiyar Kudancin Amurka.

A halin yanzu babu wata rigakafi ko maganin musamman da aka amince da shi domin cutar hantavirus, lamarin da ya sa kariya ta hanyar yaki da beraye da kula da tsafta ke da matukar muhimmanci.

NCDC ta bukaci ‘yan Najeriya da su rika dogaro da sahihan bayanan lafiya kawai tare da kai rahoton duk wata damuwa ta hanyar layin wayar kyauta mai lamba 6232, tana mai jaddada cewa yin taka-tsantsan da kariya su ne mafi ingancin kariya daga cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *