Trends

Jihar Legas Ta Kaddamar da Tsarin Tallafin Kiwon Lafiya na Shekaru 10

Babajide Sanwo- Olu, Gwamnan Lagos

Lagos State Primary Health Care Board ta kaddamar da sabon tsarin tallafin harkokin kiwon lafiya na shekaru 10 domin karfafa samar da kudade, inganta gaskiya wajen gudanarwa, da tabbatar da dorewar ayyukan kiwon lafiya a fadin jihar.

An bayyana shirin ne yayin taron Conference 57, wani taro na kwanaki biyu da aka gudanar a Ibeju-Lekki, inda jami’an lafiya, shugabannin kananan hukumomi da abokan hulda suka tattauna matsalolin da ke tattare da tallafin kiwon lafiya tare da gabatar da hanyoyin warware su na dogon lokaci.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Akin Abayomi, ya ce tsarin shekaru 10 zai taimaka wajen tsara ci gaban bangaren kiwon lafiya yadda ya kamata tare da tabbatar da dorewarsa.

“Tsarin ci gaba na shekaru 10 mai fayyace manufofi zai ba mu damar tsara bangaren kiwon lafiyarmu yadda zai samar da ci gaba mai ma’ana da dorewa. Hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da kananan hukumomi na da matukar muhimmanci,” in ji shi.

Wakilin Association of Local Governments of Nigeria (ALGON), Abdullahi Olowa, ya bayyana cewa rawar da kananan hukumomi za su taka na da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar shirin domin amfanin ya kai kai tsaye ga al’umma.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar, Ibrahim Mustafa, ya bayyana kiwon lafiya na matakin farko a matsayin ginshikin tsarin lafiya na jihar Legas, yana mai jaddada muhimmancin amfani da kayan aiki da kudade yadda ya kamata.

“Dole ne mu tabbatar cewa albarkatun da aka ware ba kawai sun isa ba ne, har ma ana gudanar da su cikin gaskiya da inganci,” in ji shi.

Daga cikin hanyoyin samar da kudaden da aka bayyana akwai Basic Healthcare Provision Fund da kuma fadada shirin inshorar lafiya na Ilera Eko, wanda aka tsara domin kara bai wa mazauna jihar damar samun kulawar lafiya da kariyar kudi.

Taron ya kuma mayar da hankali kan matsalolin tsarin gudanarwa da suka hada da yadda ake rabon albarkatu, fadada ayyukan lafiya zuwa matakin karkara, da kuma inganta gudanar da ayyuka.

Lagos State Primary Health Care Board ta sake tabbatar da kudirinta na aiwatar da tsarin, tana mai cewa zai zama jagora wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya a jihar Legas cikin shekaru goma masu zuwa, tare da mayar da hankali kan gaskiya da hadin gwiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *