Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da kamfanin kera jiragen sama na Turai, Airbus, domin samar da tsarin kula da lafiya na gaggawa ta jiragen sama a fadin kasar.
Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Jama’a na Tarayya, Muhammad Pate, ya kai ziyara kasar Faransa a wannan mako domin duba kayayyaki da fasahohi, bayan samun amincewar Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
Sabon tsarin da ake shirin samarwa zai hada ayyukan motocin asibiti na sama da tsarin kula da lafiya na kasa da ke kasa, tare da mayar da hankali kan yankunan da ke da wahalar isa da kuma wadanda ba su da isasshen kulawa.
A cewar wata sanarwa, Pate ya gudanar da ganawa da manyan jami’an kamfanin Airbus, sannan ya ziyarci jirgin saukar ungulu na agajin gaggawa a wani cibiyar kula da lafiya da gwamnatin Faransa ke tallafawa a birnin Lyon.
Ya bayyana cewa gwamnati na fadada kayayyakin more rayuwa na lafiyar jama’a da na masu zaman kansu domin inganta samun kulawar gaggawa.
Ya ce, “Muna sake fasalin Shirin Kasa na Ayyukan Gaggawa da Motocin Asibiti (NEMSAS) domin inganta yadda ake kai dauki a birane da karkara.”
Shirye-shiryen sun hada da samar da tsarin motocin asibiti na karkashin kasa a birane, da kuma karfafa ayyukan gaggawa a karkara, tare da shirye-shiryen daukar mata masu juna biyu kamar amfani da keke uku (tricycle ambulances) a yankunan da ke da nisa.
A baya-bayan nan, jihohi da dama sun bullo da irin nasu tsare-tsare, ciki har da na jihar Kaduna (KADSEMSAS) da na jihar Anambra (ASEMSAS), wadanda ke samar da hidimar gaggawa na sa’o’i 24 tare da cibiyoyin karbar kira, motocin asibiti da kuma horar da ma’aikata.
A matakin tarayya kuwa, ana ci gaba da fadada NEMSAS domin tabbatar da cewa ana kai daukin likita cikin gaggawa a cikin awanni 48 na farko, a wani bangare na gyaran tsarin kiwon lafiya na gaggawa a Najeriya.
