Trends

Cutar Koda na Ƙaruwa a Arewa-Maso-Gabas, Masana Sun Yi Gargaɗi

Masana kiwon lafiya sun yi gargaɗi kan yadda cutar koda ke ƙaruwa a yankin Arewa-Maso-Gabas na Najeriya, inda suka kiyasta cewa mutum ɗaya cikin kowane mutum 30 na fama da ita a yankin.

An bayyana wannan ne yayin shirye-shiryen gwajin lafiya kyauta da Hukumar Raya Yankin Arewa-Maso-Gabas (NEDC) ta shirya a jihohin Gombe da Bauchi.

Likitan ƙwararren kula da cututtukan koda na yara, Dakta Ali Razak, ya ce manufar shirin ita ce ƙarfafa gano cutar da wuri.

Ya ce, “Gano cutar da wuri yana da matuƙar muhimmanci wajen rage matsaloli,” tare da gargadin jama’a da su guji shan magunguna ba tare da shawarar likita ba, domin hakan na iya lalata koda.

Razak ya bayyana cewa cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, gudawa, da rashin ruwa a jiki su ne manyan dalilan kamuwa da cutar a yara, yayin da hawan jini da ciwon sukari ke haddasa ta a manya.

Ya jaddada cewa rigakafi da wayar da kai suna da matuƙar muhimmanci wajen rage yawaitar cutar.

A jihar Bauchi, NEDC ta haɗa gwiwa da Ƙungiyar Likitocin Koda ta Najeriya wajen gudanar da yaƙin wayar da kai a Tashar Mota ta Tashan Mass.

Mai kula da shirin a jihar, Alhaji Aliyu Isiyaku, ya ce an tsara wannan shiri ne domin ƙara sauƙaƙa samun gwajin lafiya da kuma ilmantar da jama’a kan hanyoyin rigakafi.

Shugaban Cibiyar Kula da Koda a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Dakta Mohammed Rabi’u Garba, ya danganta ƙaruwa da cutar da munanan halayen rayuwa, gurɓataccen muhalli, da kuma amfani da magungunan gargajiya ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ƙara da cewa mutanen da ke aiki a yanayi mai tsanani, musamman masu fuskantar zafi da rashin ruwa a jiki, na cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Garba ya bayyana cewa duk da cewa kuɗin wankin koda (dialysis) ya ragu zuwa kusan naira 12,000 a kowane zama, kula da cutar koda har yanzu yana da tsada.

Ya kuma bayyana cewa kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na marasa lafiya na da wasu cututtuka kamar hawan jini ko ciwon sukari, wanda ke nuna muhimmancin ɗaukar matakan rigakafi.
An bayar da gwaje-gwaje kyauta da kuma magunguna na farko ga jama’a a yayin shirin, yayin da aka tura masu matsaloli masu tsanani zuwa asibitoci domin ƙarin kulawa.