Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta sake jaddada aniyarta na tabbatar da tsaro, inganci da tasirin kayayyakin da ake samarwa daga tsirran magani da na ƙamshi a Najeriya.
Daraktar Janar ta hukumar, Mojisola Adeyeye, ta bayyana hakan a yayin taron #BeWildForNature Youth Network da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ya shirya domin bikin Ranar Dabbobin Daji ta Duniya a Abuja.
Adeyeye, wadda Chizoba Maduagwuna, Mataimakiyar Darakta kan Hulɗa da Ƙasashen Waje da Kasuwanci ta wakilta, ta ce aikin NAFDAC ya haɗa da kula da abinci, magunguna, kayan kwalliya, sinadarai, na’urorin lafiya da kuma magungunan gargajiya.
Ta jaddada cewa dole ne dukkan kayayyakin da ake samarwa daga tsirrai su cika ƙa’idojin tsaro da inganci masu tsauri.
Adeyeye ta bayyana muhimmancin tsirran magani tun a tarihi a matsayin hanyoyin warkarwa da kuma ginshiƙin al’adu, tana mai cewa suna ƙara zama muhimmai a hanyoyin kiwon lafiya na zamani.
Ta ce, “Manufarmu ita ce mayar da albarkatun halittu zuwa kayayyaki masu aminci da aka tantance tare da samar da damar tattalin arziki, yayin da ake kare lafiyar jama’a.”
Ta kara da cewa tsirran magani wata babbar dukiya ce ta ƙasa da za ta iya tallafa wa masana’antu na cikin gida tare da ƙarfafa tattalin arzikin halittu (bio-economy) na Najeriya.
NAFDAC na tabbatar da cewa magungunan tsirrai (phytomedicines), man ƙamshi (essential oils), sinadaran gina jiki (nutraceuticals), da kayan kwalliya suna bin ƙa’idojin tasiri da inganci.
Adeyeye ta kuma jaddada cewa tsirran magani na da babbar damar samar da ayyukan yi masu ɗorewa, musamman a yankunan karkara, tare da bai wa mata da matasa damar samun ci gaba.
Ta ce muhimman matakan da ake ɗauka sun haɗa da noman tsirrai cikin kulawa, kare albarkatun halittu, daidaita ƙa’idoji, bincike, da haɗin gwiwa da jami’o’i da masana’antu.
Ta kuma ambaci wasu shirye-shirye kamar Kwamitin Magungunan Gargajiya na Najeriya, Jerin Muhimman Tsirran Magani, da Littafin Ka’idojin Magungunan Tsirrai a matsayin ginshiƙai na tsarin kula da su.
Haka kuma, an jaddada wayar da kan jama’a kan yadda za a yi amfani da tsirran cikin aminci da kuma kasuwancinsu ta hanyar da ta dace.
A ƙarshe, Adeyeye ta yi gargadin cewa albarkatun halittu na Najeriya wata babbar kadara ce da dole a kare ta ta hanyar bin hanyoyin dorewa da ƙa’idoji masu ƙarfi.
Ta sake tabbatar da cewa NAFDAC za ta ci gaba da ƙarfafa bincike da kuma tabbatar da amfanin tsirran magani cikin aminci a fannoni daban-daban na rayuwa.
