Trends

Bukin Easter: Gwamnatin Tarayya Ta Ayana Juma’a da Litinin Ranar Hutu

Olubunmi Tunji-Ojo Ministan cikin gida

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, da Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, a matsayin ranakun hutu domin bikin Easter na wannan shekara.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba.

Ya taya Kiristoci a Najeriya da ma na ƙasashen waje murnar bikin Easter, yana mai bayyana shi a matsayin lokaci na tunawa da sadaukarwa, ƙauna, da sabuwar rayuwa.

Tunji-Ojo ya buƙaci ‘yan Najeriya su rungumi kyawawan dabi’u kamar sadaukar da kai, yafiya, haƙuri, da ƙauna, kamar yadda aka gani a rayuwa da koyarwar Yesu Almasihu.

Ministan ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ƙarfafa haɗin kan ƙasa ta hanyar haƙuri da juna da kuma gina kyakkyawar al’umma.

Yana mai jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaban ƙasa, ya ce manufofi da matakan da ake ɗauka a halin yanzu na nufin samar da bunƙasar tattalin arziki, sabuwar farfaɗowar ƙasa, da wadata ga kowa.

Sanarwar, wadda Sakatare na dindindin a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu, ta yi wa dukkan Kiristoci fatan samun bikin Easter cikin lumana da farin ciki.