Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na bunkasa noman shinkafa, inda ta tura jami’ai zuwa jihohi 13 na gwaji domin karfafa sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan noma.
Matakin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa manoma sama da 3,500 sun yi watsi da noman shinkafa a lokacin rani na shekarar 2026, inda aka yi asarar da ta kai kimanin naira biliyan 93.
An tsara shirin ne karkashin jagorancin Sashen Shugaban Kasa mai kula da Tsarin Abinci da kuma Ma’aikatar Noma ta Tarayya, inda aka gudanar da horo ga wakilan jihohi a cibiyar National Agricultural Extension and Research Liaison Services da ke Zariya.
Mataimakin Darakta, Tunji Iyiola-Tunji, ya bayyana cewa sahihan bayanai daga filayen noma sun nuna cewa manoma na rage yawan noman shinkafa.
“Kafin a yanke hukunci a matakin kasa, dole ne gwamnati ta fahimci yadda manoma ke amfani da damar yanayi da kuma sakonnin da suke aikawa ta hanyar ayyukansu,” in ji shi.
Binciken da ya shafi manoma 33,507 ya nuna cewa kusan kashi 10.6% na shirin rage noman shinkafa, wanda ya kai kusan manoma 3,500.
Yawancin manoman sun koma noman waken soya da ridi (sesame), saboda karin riba da kuma bukatar da ake da ita a kasuwannin duniya.
Rahoton Babban Lokacin Damina na 2025 ya nuna cewa an yi asarar naira 20,220 a kowace hekta ta shinkafa, yayin da samar da shinkafa ya ragu da kashi 7.9%, masara da kashi 2.8%, da dawa da kashi 1%, a lokaci guda kuma noman waken soya ya karu da kashi 38%.
Mai kula da shirin NAPM, Marion Moon, ta yi gargadin cewa ribar da ake samu daga ridi na iya zama ta dan lokaci.
“Idan kowa ya koma noman ridi, farashinsa zai fadi, ribar kuma za ta ragu,” in ji ta.
Kwamitin ya ba da shawarar kaddamar da Shirin Ceto Noman Rani na shinkafa da masara, wanda zai hada da tallafin kayan noma, taimakon ban ruwa, da samar da tsare-tsaren kudade domin daidaita samar da abinci da kuma hana manoma komawa ga amfanin gona na fitar da kaya waje.

