Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gwamnatocin jihohi na daukar kusan kashi 48 cikin 100 na dukkan kashe-kashen kudaden gwamnati a Najeriya, lamarin da ke nuna bukatar inganta hadin kai tsakanin dukkan matakan gwamnati.
Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ne ya bayyana hakan yayin da yake maraba da sabuwar Karamin Ministar Ma’aikatar, Doris Uzoka-Anite, a ma’aikatar da ke Abuja.
Bagudu ya jaddada cewa daidaita manufofi tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi na da matukar muhimmanci wajen cimma manufofin ci gaban kasa.
“Gwamnatocin jihohi na daukar kusan kashi 48 cikin 100 na dukkan kashe-kashen gwamnati,” in ji shi, yana mai nuni da tattaunawar da aka yi a National Economic Council.
Ya kuma sake jaddada burin gwamnatin na bunkasa tattalin arzikin Najeriya zuwa dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030, ta hanyar samun ci gaba na kusan kashi 7 cikin 100 a kowace shekara, karkashin sabon shirin ci gaban kasa na 2026 zuwa 2030.
Muhimman bangarorin da za a mayar da hankali a kai sun hada da zuba jari a tsaro, samar da kudaden gina manyan ababen more rayuwa, da kuma dakile ayyukan haram a bangaren hakar albarkatun kasa kamar satar danyen mai da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Bagudu ya kuma bayyana cewa kyautata alakar Najeriya da China ta haifar da sabbin yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
A nata bangaren, Uzoka-Anite ta jaddada muhimmancin bangaren masu zaman kansu, inda ta ce, “Kusan kashi 95 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin Najeriya dole ne bangaren masu zaman kansu su jagoranta, yayin da gwamnatin tarayya za ta bada kashi 5 cikin 100 kacal.”
Ta bukaci a gina shirin “Renewed Hope” bisa jagorancin bangaren masu zaman kansu, tana mai cewa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya shimfida tubalin cimma burin tattalin arzikin dala tiriliyan 1 ta hanyar gyare-gyare da shirin ci gaban kasa.
Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Deborah Odoh, ta bayyana cewa zuwan Uzoka-Anite ya zo a kan lokaci, inda ta ce kwarewarta a kwamitocin tattalin arziki za ta kara karfafa jagorancin ma’aikatar wajen aiwatar da manufofin shugaban kasa.



