Najeriya Ta Yi Mu’amalar Kudin Crypto ta Dala Biliyan 96 – SEC

Hukumar Kula da Harkokin Zuba Jari da Kasuwannin Kudi ta Securities and Exchange Commission Nigeria ta bayyana cewa tsarin hada-hadar kudi na zamani a Najeriya ya kai kusan dala biliyan 96 a mu’amalolin kudaden crypto da sauran kadarorin dijital.

Daraktan Janar na hukumar, Emomotimi Agama, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tuntuba da ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja. Ya jaddada cewa girman wadannan mu’amaloli na bukatar karin tsauraran matakan sa ido.

“A halin yanzu… harkokin cryptocurrency na kai kusan dala biliyan 96 a Najeriya, kuma hakan na da muhimmanci a gare mu mu tsara yadda za mu sarrafa shi yadda ya kamata,” in ji shi.

Ya bayyana cewa sabuwar dokar Investment and Securities Act 2025 ta kara karfafa ikon SEC wajen tsara dokoki kan kadarorin dijital, sa ido kan hadurran tsarin kudi, da kuma daidaita kasuwar jari ta Najeriya da ka’idojin duniya.

Agama ya kara da cewa kasuwar jari ta amince da sabbin takardun zuba jari da suka kai kimanin naira tiriliyan 3.68 a shekarar 2024, wanda ya taimaka wajen bunkasa zuba jari a hannun jari da kuma bashin gwamnati da kamfanoni.

Haka kuma, sama da bankuna 31 sun samu damar tara kudade a wani bangare na sake karfafa jarin bankuna.
A bangaren ci gaban kasuwa, darajar kasuwar jari ta tashi daga naira tiriliyan 55 a 2024 zuwa naira tiriliyan 127, yayin da gudunmawarta ga tattalin arzikin kasa (GDP) ta karu daga kashi 13 zuwa kashi 33.

Hukumar SEC ta kuma kara kaimi wajen kare masu zuba jari, inda ta fitar da gargadi sama da 90 kan zamba da tsare-tsaren damfara, tare da hada kai da ‘yan sanda wajen dakile ayyukan Ponzi.

Agama ya jaddada muhimmancin kasuwar jari wajen samar da kudaden gina ababen more rayuwa ta hanyar bashin jihohi da kuma tallafawa bangaren gidaje ta hanyar Asusun Mortgage Refinancing and Infrastructure Fund.

A gaba, ya ce SEC na da burin kara zurfafa kasuwar jari, ta yadda za a kara yawan darajarta idan aka kwatanta da GDP kamar yadda ake samu a kasashe masu tasowa irin su India, tare da fadada kariyar zamantakewa domin tabbatar da cewa sauye-sauyen suna anfani ga talakawan Najeriya.