Trends

Zazzabin Lassa: NCDC Ta Ɗaga Ƙararrawa Kan Ƙaruwar Cuta a Jihohi 18

Hukumar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Ƙasa (NCDC) ta nuna damuwa kan yadda cutar zazzabin Lassa ke ƙaruwa a jihohi 18 da ƙananan hukumomi 67 a faɗin Najeriya.

Hukumar ta danganta ci gaba da yaɗuwar cutar da ƙarin mace-mace da gibin da ake da shi a matakin jihohi wajen aiwatar da matakan dakile ɓarkewar cuta, tana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa domin ƙarfafa tsarin yaki da ita.

Daraktan-Janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Ya ce jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Edo da Benue ne suka fi ɗaukar kaso mafi yawa, inda suka kai sama da kashi 80 cikin ɗari na tabbatattun masu cutar da aka samu a lokacin kololuwar yaɗuwar cutar a shekarar 2026.

Idris ya bayyana cewa abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda cutar ke ƙaruwa tsakanin ma’aikatan lafiya, inda aka tabbatar da kamuwa 28 tare da mutuwar mutum uku a wannan kakar.

Ya ce binciken da aka gudanar a wurare ya nuna cewa yawancin kamuwa da cutar na faruwa ne a yankunan da aka saba da cutar, amma gazawar aiwatar da tsare-tsaren da aka tanada na dakile ta ya taimaka wajen ci gaba da yaɗuwarta da kuma ƙara yawan mace-mace.

A cewarsa, daga cikin gibin da aka gano akwai kamuwa da cutar a sassan kula da marasa lafiya na waje da kuma dakunan haihuwa, rashin bin ƙa’idojin Kariya da Dakile Kamuwa da Cuta (IPC), da kuma rashin wadatattun kayan kariya na ma’aikata (PPE).

Ya ƙara da cewa jinkirin zuwa asibiti sakamakon matsalolin kuɗi, rashin daidaitaccen kunna Tsarin Gudanar da Lamarin Gaggawa na Jihohi, raunin bin diddigin masu hulɗa da marasa lafiya, tsangwama daga al’umma, da kuma rashin ingancin cibiyoyin killacewa na daga cikin abubuwan da ke ƙara yaɗuwar cutar.

Idris ya jaddada cewa aiwatar da matakan dakile ɓarkewar cuta da kuma isar da ayyukan kiwon lafiya na karkashin alhakin gwamnatocin jihohi ne a tsarin tarayyar Najeriya, yana mai kira gare su da su ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma ware isassun kuɗaɗe.

Ya buƙaci jihohin da cutar ta shafa da ma waɗanda ke cikin haɗari da su hanzarta kunna Tsarin Gudanar da Lamarin Gaggawa tare da sanya ido sosai domin tabbatar da haɗin kai da ingantaccen aiki a dukkan matakan kula da lafiya.

Haka kuma ya yi kira da a gaggauta sakin kuɗaɗen yaki da cutar, a tsaurara bin ƙa’idojin IPC a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu, tare da tabbatar da wadatar PPE da sauran kayan aiki masu muhimmanci.

Shugaban NCDC ya kuma ba da shawarar ƙarfafa hanyoyin tallafin kuɗi ga marasa lafiya domin rage jinkirin zuwa asibiti da yawan mace-mace, tare da ɗaukar matakan yaƙi da beraye da tsaftar muhalli a ƙarƙashin tsarin “One Health”.

Ya shawarci ma’aikatan lafiya da su kasance masu sa ido sosai kan alamun cutar tare da bin ƙa’idojin IPC ba tare da sakaci ba.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su kiyaye tsaftar muhalli, su hana beraye shiga gidajensu, su adana abinci yadda ya kamata, tare da neman kulawar likita da wuri idan alamun cutar sun bayyana.

Idris ya bayyana cewa ana iya warkar da zazzabin Lassa idan an gano shi da wuri, yana mai cewa Najeriya na kuma fuskantar wasu cututtuka masu saurin ɓarkewa kamar sankarau (Cerebrospinal Meningitis), Diphtheria, Mpox da kwalara.

Ya sake tunatar da al’umma da layin gaggawa na NCDC mai lamba 6232, wanda ba a biya kuɗi, domin kai rahoton zargin kamuwa da cutar ko neman ƙarin bayani.