Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na zuba jari a bangaren sufurin jiragen sama, inda take shirin kafa tsarin aerotropolis — wato hada filayen jiragen sama da biranen kasuwanci, cibiyoyin sufuri da masana’antu — a manyan biranen kasar nan.
Ana sa ran kaddamar da shirin a taron Aircraft Acquisition and Investment Summit mai zuwa, wanda zai hada manyan kamfanonin bayar da jiragen haya, masu zuba jari, bankuna da kamfanonin jiragen sama daga sassa daban-daban na duniya domin tattaunawa kai tsaye da ‘yan kasuwar Najeriya.
Michael Achimugu, Daraktan Hulda da Jama’a da Kare Hakkin Fasinja na Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA), ya bayyana shekarar 2026 a matsayin shekara mai muhimmanci ga ci gaban harkar sufurin jiragen sama a Najeriya.
Ya ce, “Muna kawo manyan ‘yan wasa na duniya; kamfanonin bayar da jiragen haya, bankuna, masu zuba jari da masu daukar nauyin kudi domin su zauna kai tsaye da masu harkar jiragen sama da sauran ‘yan kasuwa a cikin tsarin sufurin jiragen sama na Najeriya.”
Ana sa ran taron zai ja hankalin manyan kamfanonin bayar da jiragen haya, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, da masu zuba jari da ke neman shiga kasuwar sufurin jiragen sama ta Najeriya wadda ke ci gaba da bunkasa cikin sauri.
Tun da farko, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya jagoranci wata tawaga zuwa taron Airline Economics Growth Frontiers Conference da aka gudanar a Dublin a shekarar 2025, inda Najeriya ta tattauna da masu ruwa da tsaki na duniya kan sabunta jirage, samar da rancen kudi mai sauki, da kuma ingantattun hanyoyin gudanar da aiki masu dorewa.
Keyamo ya ce tattaunawar da aka yi da manyan kamfanonin jiragen sama na duniya ta tabbatar da cewa Najeriya na daya daga cikin kasuwannin sufurin jiragen sama mafi jan hankali a duniya.
“Muna daya daga cikin kasuwannin jiragen sama mafi nagarta a duniya, kuma masu zuba jari da dama na neman damar shigowa,” in ji shi.
Achimugu ya kara da cewa, baya ga samar da kudi, taron zai zama farkon aiwatar da tsarin aerotropolis wanda zai mayar da filayen jiragen sama cibiyoyin tattalin arziki da za su bunkasa kasuwanci, yawon bude ido, jigilar kaya da samar da ayyukan yi.
Ya ce shigo da sabbin jirage na haya na zamani zai taimaka wajen rage farashin tikitin jirgi, rage yawan jinkiri ko soke jirage, da kuma inganta jin dadin fasinjoji, wanda hakan zai bude sabon babi a ci gaban sufurin jiragen sama a Najeriya.


