Trends

Zaɓen FCT: PDP Ta Yi Watsi da Sakamakon AMAC

Hon. Loveth Izekor yayin taron ta da manema labarai a Abuja

Hon. Loveth Izekor, ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ƙananan Hukumomin FCT da aka gudanar a ranar Asabar, inda ta zargi cewa an tafka magudi a lokacin tattara sakamakon zaɓen.

Da take jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, Izekor ta bayyana takaicinta kan abin da ta kira sauya alkaluma domin fifita abokin takararta na jam’iyyar APC.

“Bayananmu sun nuna cewa mun yi nasara da rinjaye a mafi yawan rumfunan zaɓe. Amma an sauya alkaluman a lokacin tattara sakamakon domin fifita ɗan takarar APC. Muna kallon wannan a matsayin hari kai tsaye ga dimokuraɗiyya,” in ji ta.

’Yar takarar ta PDP ta jaddada cewa an yi magudi a zaɓen, tare da kira da a gaggauta yin gyaran tsarin zaɓe domin kare sahihancin ƙuri’u a Najeriya.
“Wannan lamari ya sake nuna muhimmancin yin gyaran dokokin zaɓe, ciki har da amfani da watsa sakamakon zaɓe kai tsaye (real-time transmission).

Har yanzu Najeriya na da sauran tafiya mai nisa, kuma muna buƙatar sauye-sauye cikin gaggawa domin kare martabar ƙuri’a,” in ji ta.
Duk da kalubalen da ta ce ta fuskanta, Izekor ta yaba wa magoya bayanta bisa jajircewarsu.

“Ina miƙa godiya ga magoya bayana da suka yi watsi da halin ko-in-kula da masu zaɓe suka nuna, suka tsaya tsayin daka tare da ni. Ƙoƙarinku bai tafi a banza ba,” ta ƙara da cewa.
Ta kuma sanar da cewa lauyoyinta na shirin kai ƙara kotun sauraron ƙararrakin zaɓe domin kalubalantar sakamakon.

“Ba za mu amince da wannan sakamako ba. Lauyoyinmu na shirye-shiryen shigar da ƙara, kuma za mu bi wannan lamari har zuwa ƙarshe. Mun ƙuduri aniyar karɓo haƙƙin da al’ummar City Centre suka ba mu ta hanyar ƙuri’unsu,” in ji ta.