Hukumar Kula da Bashin Gwamnati (DMO) ta sanar da shirin tara Naira biliyan 800 ta hanyar gwanjon takardun bashin Gwamnatin Tarayya (FGN bonds) na watan Fabrairu 2026, adadin da ya ninka na Fabrairun 2025 inda aka bayar da Naira biliyan 350 kacal.
A cewar sanarwar tayin bondon, za a fitar da Naira biliyan 400 na 17.95% FGN JUN 2032 (sake budewa na shekaru bakwai), Naira biliyan 300 na 19.89% FGN MAY 2033 (sake budewa na shekaru 10), da kuma Naira biliyan 100 na 19.00% FGN FEB 2034 (sake budewa na shekaru 10).
An shirya gudanar da gwanjon ne a ranar 23 ga Fabrairu, 2026, yayin da za a kammala biyan kudin saye (settlement) a ranar 25 ga Fabrairu. Wannan sabon shiri ya nuna karin Naira biliyan 450 idan aka kwatanta da Fabrairun bara, wanda ya kai karuwar kashi 128.6 cikin 100 — fiye da ninki biyu na tayin shekarar 2025.
Ba kamar bara ba, inda aka hada da takardar bashi ta shekaru biyar, gwanjon na Fabrairu 2026 ya mayar da hankali ne kan takardun shekaru bakwai da shekaru 10 kacal. Wannan na nuna kokarin gwamnati na tsawaita lokacin balagar bashi domin rage matsin sake biyan basussuka a nan gaba kadan.
Sai dai har yanzu kudin ruwa na kan gaba. Takardar shekaru bakwai na dauke da kudin ruwa na kashi 17.95 cikin 100, wanda ya dan ragu daga kashi 18.50 da aka bayar a Fabrairun 2025. Takardun shekaru 10 kuma na dauke da kashi 19.00 da 19.89 cikin 100, lamarin da ke nuna yadda yanayin kudin ruwa a Najeriya ke ci gaba da kasancewa mai tsada.
Idan aka kwatanta da watan Janairu, tayin na Fabrairu ya ragu da Naira biliyan 100 daga rikodin Naira biliyan 900 da aka fitar a Janairu, wanda ya hada da takardar FGN JAN 2035 mai kudin ruwa na kashi 22.60 cikin 100.
Raguwar kudin ruwa daga kashi 18.50 a Janairu zuwa 17.95 a Fabrairu ga takardar shekaru bakwai na nuna dan saukin da ake samu, duk da cewa har yanzu kudin ruwa na zagaye tsakanin kashi 18 zuwa 20 cikin 100, abin da ke nuna tsadar bashin cikin gida.
A dunkule, gwanjon Fabrairu ya nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da dogaro da bashin cikin gida, tare da karin adadin takardun bashi da tsawaita wa’adinsu domin daidaita bukatun kasafin kudi da kuma rage hadarin sake biyan basussuka a nan gaba.









