Fitar da Iskar Gas Waje Ta Kai Kashi 35% a 2025

Najeriya ta samar da tiriliyan 2.71 na standard cubic feet (scf) na iskar gas a shekarar 2025, inda kusan kashi 35 cikin 100 na adadin aka fitar zuwa kasashen waje, a cewar Hukumar Kula da Bangaren Man Fetur ta Sama, wato Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC).

Adadin ya zarce na shekarar 2024 wanda ya tsaya a tiriliyan 2.5 na scf. A shekarar 2025, an fitar da biliyan 942.7 na scf zuwa ketare, yayin da biliyan 780.6 na scf aka sayar a cikin gida.

Sauran biliyan 776.6 na scf kuma an yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan hakar mai a filayen mai, wanda hakan ya kai jimillar amfani da gas zuwa tiriliyan 2.5 na scf, wato kashi 92.4 cikin 100 na duk abin da aka samar.

Rahoton ya nuna cewa gas din da ke fitowa tare da mai (associated gas) ya kai tiriliyan 1.456 na scf, yayin da wanda ba ya hade da mai (non-associated gas) ya kai tiriliyan 1.25 na scf, lamarin da ke nuna kusan daidaito tsakanin hanyoyin samar da gas din.

A wata-wata, samar da gas ya fi yawa a watan Yuli inda ya kai biliyan 250.9 na scf, yayin da watan Satumba ya fi kankanta da biliyan 198.3 na scf. Fitar da gas zuwa kasashen waje ta fi yawa a watan Disamba da biliyan 101.9 na scf, amma ta ragu matuka a watan Satumba zuwa biliyan 45.4 na scf.

Sayar da gas a cikin gida ta fi karfi a watan Mayu da biliyan 73 na scf, amma ta ragu zuwa biliyan 56.1 na scf a watan Disamba.

Duk da yawan amfani da gas din, biliyan 204 na scf an kone (gas flaring) a shekarar, wanda ya kai kashi 7.5 cikin 100 na jimillar abin da aka samar.
Rahoton ya kara da cewa an fi kona gas a watan Yuli da biliyan 18.3 na scf, yayin da watan Disamba ya fi karanci da biliyan 15.4 na scf. Watan Satumba ne ya fi yawan kaso na kona gas da kashi 9.05 cikin 100.

NUPRC ta bayyana cewa alkaluman sun nuna yadda fitar da gas zuwa waje ke da rinjaye a kasuwar gas ta Najeriya, inda ya kai kashi 38 cikin 100 na dukkan gas din da aka yi amfani da shi. Ta kuma ce alkaluman karshe na zangon karshe na shekara (Q4) na iya sauyawa bayan an kammala tantancewa.

A wani bangare, hadakar kamfanonin NNPC da Heirs Energies a OML 17 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwantar da gas din da ake konewa (Gas Flare Commercialisation Agreements) a watan Oktoba, domin kama gas din da ake konewa a mayar da shi amfani wajen samar da wutar lantarki, masana’antu, iskar girki da kuma compressed natural gas (CNG), daidai da manufofin sauyin makamashi na Najeriya.