Matatar Man Fetur ta Dangote ta zargi wasu “marasa kishin ƙasa kuma marasa gaskiya” da shirya kamfen na yaɗa ƙarya da nufin lalata sunan da ayyukan matatar dala biliyan 20, tare da ci gaba da riƙe dogaron Najeriya ga shigo da fetur daga waje.
Kamfanin ya ce ana yaɗa wannan kamfen ta hanyar rahotannin da ke ruɗar da jama’a, inda ake ƙaryata gaskiya ta hanyar cewa Matatar Dangote na shigo da cikakken fetur zuwa Najeriya.
“Wannan farfaganda na fitowa ne daga marasa kishin ƙasa da marasa gaskiya waɗanda ba sa son ganin Najeriya ta daina shigo da fetur,” in ji sanarwar, inda matatar ta ƙara da cewa za ta bayyana sunayen masu hannu a kai a lokacin da ya dace.
Dangote ta kuma yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda ke bayan kamfen ɗin sun taɓa cin gajiyar kuɗaɗen bogi da aka kashe wajen gyaran matatun gwamnati da suka gaza aiki, lamarin da ya lashe biliyoyin kuɗi ba tare da dawo da samarwa ba.
Matatar ta amince cewa tana shigo da wasu kayayyakin shigarwa (feedstocks) da sinadaran gauraya mai kamar reformates da condensates, amma ta jaddada cewa ba cikakken fetur ba ne, illa matakan tsaka-tsaki da ke buƙatar ƙarin tacewa kafin su cika ƙa’idojin kasuwa.
“Dole ne waɗannan kayayyaki su ƙara shiga matakan tacewa kafin su dace da ƙa’idojin kasuwa,” in ji kamfanin, yana ƙara da cewa wannan al’ada ce da ake yi a Turai da Asiya.
Sai dai masu suka sun fitar da wadannan shigo-shigo a matsayin fetur da aka gama, suna cewa Dangote na sake shirya fetur ne kawai maimakon tace ɗanyen mai. Matatar ta ƙi amincewa da hakan, tana kiran zargin “ƙarya kuma mai ruɗarwa,” tana mai cewa an yi shi ne don rikitar da fahimtar jama’a da kuma rage amincewa da cigaban tace mai a cikin gida.
Rikicin ya sake nuna tashin hankali da ke kewaye da matatar mai mai iya tace ganga 650,000 a rana, wadda ita ce matar mai guda ɗaya mafi girma a Afirka, kuma wadda ke barazana ga tsofaffin masu anfani a harkar shigo da fetur. Tsawon shekaru, ’yan tsaka-tsaki masu alaƙa da siyasa sun ci gajiyar shigo da fetur, yayin da matatun gwamnati ke tsaya cak.
A wani taron S&P Global da aka gudanar a Birtaniya, matatar ta yi karin bayani kan ayyukanta, tana jaddada cewa fetur da take samarwa ga Najeriya ya cika ƙa’idar Euro 5, kuma yana wuce tsauraran gwaje-gwajen inganci.
Wannan, a cewar ta, babban sauyi ne idan aka kwatanta da fetur mai ƙazanta da sinadarin sulphur mai yawa da Najeriya ta saba shigowa da shi a baya.
A ƙarshe, Dangote ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a masana’antar mai da kafafen yaɗa labarai da su ɗaga matakin sahihanci na fasaha, daidaito da ɗaukar alhaki a rahotanninsu, tana jaddada rawar da matatar ke takawa wajen sauya fasalin sashen man fetur na Najeriya da kuma rage dogaro da shigo da fetur daga waje.
