Trends

Najeriya za ta Rage Karɓar Bashi, ta Ƙarfafa Tattara Kuɗaɗen Ciki Gida — Edun

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziƙi na Ƙasa, Wale Edun, ya ce dole ne Najeriya ta rage dogaro da karɓar bashi tare da ƙarfafa tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida, domin daidaita harkokin kuɗi da kuma tallafa wa ci gaba mai ɗorewa.

Edun ya bayyana haka ne a taron horaswa na shugabannin Hukumar Haraji ta Ƙasa (Nigerian Revenue Service) da aka gudanar a Abuja, inda ya yi gargaɗi cewa yanayin kuɗaɗen duniya ya tsananta ga ƙasashe masu tasowa, lamarin da ya sa karɓar bashi ya zama mai tsada kuma mara ɗorewa.
“Dole ne mu rage dogaronmu ga bashi. Tattara kuɗaɗen shiga a wannan yanayi wajibi ne na ci gaba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa a shekarar 2024, ƙasashe masu tasowa sun biya dala biliyan 163 wajen biyan bashin da ke kansu, alhali tallafin ƙasashen waje ya tsaya a dala biliyan 42, yayin da zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje ya kai dala biliyan 97. A cewarsa, wannan ya nuna cewa tushen kuɗaɗen waje ya fara raguwa.

“Wannan gaskiya na nufin cewa Najeriya dole ta jingina dorewar kasafin kuɗinta da ƙarfin tara kuɗaɗen shiga na cikin gida, maimakon ci gaba da dogaro da bashi a zamanin ribace-ribacen bashi masu tsada,” in ji Edun.

Ministan ya danganta matsin bashin Najeriya da girgizar tattalin arziƙin duniya kamar annobar COVID-19, rikice-rikicen siyasa na duniya, da takaddamar kasuwanci, waɗanda suka tilasta wa ƙasashe da dama ƙara karɓar bashi tare da ƙarin kuɗin biyan sa.

Ya jaddada cewa kuɗaɗen shiga masu ɗorewa su ne ginshiƙin gina ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da kuma tallafa wa ƙungiyoyin da suka fi rauni a al’umma.

Duk da cewa Majalisar Dattawa ta nuna cewa karɓar bashi na da wuya a kauce masa domin cike gibin kasafin kuɗi, Edun ya nace cewa gyaran haraji ne mabuɗin rage dogaro da bashi. Ya ƙara da cewa bin doka da amincewa da tsarin haraji na da matuƙar muhimmanci.

“Mutane dole su ga amfanin gudummawar da suke bayarwa ta hanyar ayyuka da hidimomi,” in ji shi.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa, Zacch Adedeji, ya ce dole ne hukumar ta samar da sakamako a aikace, ba wai rubuce-rubucen gyare-gyare kaɗai ba.

“Abin da ya kawo mu nan ba zai wadatar da inda muke nufi ba,” in ji Adedeji, yana kira ga shugabanni da su rungumi alhaki da tsari mai tsauri.