‘Yan Najeriya sun cire naira tiriliyan 36.34 ta hanyar injinan cire kudi ta atomatik (ATM) tsakanin watan Janairu da Yuni na shekarar 2025, abin da ke nuna karin kashi 197.66 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar 2024, duk da sabbin kudaden cire kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bullo da su.
Wannan karuwar na nuni da cewa har yanzu ana amfani da kudi sosai a kasar, inda mu’amalar ATM ta kusan ninka sau uku idan aka kwatanta da bara.
An samu karin cire kudi ta ATM a dukkan watanni shida, inda watan Mayu ya fi daukar hankali da mafi yawan kudin da aka cire, wanda ya kai naira tiriliyan 7.44 a wata guda.
Yawan mu’amaloli ma ya karu da kashi 72.98 cikin 100, inda ya kai miliyan 858.80, lamarin da ke nuna cewa karin kudin cajin cire kudi bai hana mutane amfani da ATM ba.
Sabon tsarin cajin kudi na CBN, wanda ya fara aiki a watan Fabrairu 2025, ya tanadi cajin naira 100 kan duk naira 20,000 da aka cire daga ATM na wani banki dabam, tare da karin cajin musamman idan ATM din yana wajen harabar banki.
Duk da haka, ‘yan Najeriya sun ci gaba da dogaro da ATM wajen mu’amalolinsu, abin da ke nuna muhimmancin amfani da kudi a harkokin tattalin arzikin yau da kullum.
A gefe guda kuma, mu’amalar na’urorin saye da biyan kudi (POS) na ci gaba da yin rinjaye ta fuskar adadin kudade, inda darajarsu ta karu daga naira tiriliyan 85.91 a rabin farkon shekarar 2024 zuwa naira tiriliyan 147.20 a rabin farkon shekarar 2025.
Sai dai, saurin karuwar mu’amalar ATM ya zarce na POS, lamarin da ke kara nuna ci gaba da muhimmancin kudi a hannun jama’a.
CBN ta danganta wannan karuwar mu’amalar ATM da karin kudaden gudanarwa da kuma kokarin inganta inganci. Haka kuma, bankin ya umarci bankuna da su kara girka injinan ATM domin fadada samun su ga jama’a da kuma rage dogaro da wakilan POS.
