Trends

Kotu Ta Dakatar da PENGASSAN Daga Yunkurin Katse Iskar Gas Zuwa Kamfanin Mai Dangote

Mai shari’a Emmanuel Subilim na Kotun Kwadago ta Ƙasa dake Abuja, ya hana Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) aiwatar da shirin yin yajin aikin da ta tsara kan Kamfanin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals FZE.

A cikin hukuncin da ya yanke bisa roƙon gaggawa da kamfanin Dangote ya gabatar, Mai shari’a Subilim ya hana masu kare kara, ciki har da Nigeria National Petroleum Company Ltd (NNPCL), Nigeria Midstream and Downstream Petroleum, da Nigeria Upstream Petroleum Regulatory Commission, daga katse iskar gas da kuma man da ake kaiwa wa masana’antar Dangote.

Babban Lauya, George Ibrahim (SAN), shi ne ya gabatar da buƙatar kamfanin Dangote a gaban kotu, inda ya samu nasarar samun umarnin hana daukar matakin.

Ibrahim ya bayyana cewa mai gabatar da ƙarar (Dangote Refinery) kamfani ne da aka ba lasisin samarwa da rarraba man fetur da kayayyakin petrochemicals don amfanin jama’ar Najeriya, kuma aikinsa na daga cikin aiyukan dole da suka da muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasa da rayuwar al’umma.

Ya ce, a ‘yan kwanakin baya, an samu wasu matsaloli na lalata kayayyaki da wasu ma’aikatan kamfanin suka yi a masana’antar, abin da ya haifar da damuwa kan lafiyar al’umma da tsaron rayuka.

Dangane da haka, shugabancin kamfanin ya yanke shawarar sake tsari a masana’antar, wanda ya haddasa sallamar wasu ma’aikata, lamarin da aka sanar da duka ma’aikata ta wata sanarwa ranar 25 ga Satumba, 2025.

Sai dai a safiyar ranar Juma’a, 26 ga Satumba, 2025, kamfanin ya samu wani rahoto a shafukan sada zumunta cewa an kore ma’aikatan Najeriya sama da 800 saboda shiga ƙungiyar PENGASSAN.

Shugabancin kamfanin ya musanta wannan zargi ta hanyar wata sanarwa ga manema labarai, inda ya jaddada cewa bai da matsala da ma’aikata shiga ƙungiya domin hakan na daga cikin ‘yancin kundin tsarin mulki. Duk da haka, ya bayyana cewa kamfanin na da ma’aikata ‘yan Najeriya sama da 3,000, kuma ƙalilan ne kawai abin ya shafa sakamakon sake tsari da matsalar tsaro.

Babban lauyan ya kuma ce, ta cikin wata wasika da aka rubuta ranar 26 ga Satumba, 2025, kuma aka yada a shafukan intanet, sakataren ƙungiyar PENGASSAN, Kwamared Lamumba Ighotemu Okugbawa, ya rubuta wa Ministan Man Fetur da Iskar Gas cewa ƙungiyar za ta dauki matakin da zai durƙusar da kamfanin Dangote idan bai dawo da ma’aikatan da aka sallama ba.

A cikin hukuncin nasa kan roƙon gaggawa, Mai shari’a Subilim ya ce da zarar aka fara yajin aikin, zai yi barna ga harkokin kamfanin, kuma hakan zai iya durƙusar da samar da ayyukan dole ga jama’ar Najeriya.

Ya ce saboda adalci, ya dace kotu ta dakatar da masu kare ƙara domin kiyaye zaman lafiya a masana’antu da kuma ci gaba da samar da ayyukan dole ga al’umma har sai an saurari shari’ar gaba ɗaya.

Mai shari’a Subilim ya bayar da umarnin hana daukar matakin na tsawon kwanaki bakwai kacal, sannan ya umurci a isar da takardun umarnin tare da motion on notice ga masu kare ƙara nan take.

Daga ƙarshe, kotun ta dage sauraron ƙarar gaba ɗaya zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2025.