Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, a matsayin hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya ‘yan Najeriya murna – duka waɗanda ke gida da kuma waɗanda ke ƙasashen waje – a wannan muhimmiyar rana ta tarihi.
Tunji-Ojo, cikin wata sanarwa da sakatariyar dindindin ta ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar, ya ja hankalin ‘yan ƙasa da su ci gaba da rungumar ƙaunar ƙasa, haɗin kai da juriya waɗanda suka ci gaba da ɗaukaka Najeriya tun daga samun ‘yancin kai a shekarar 1960.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da gaskata da shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu, wanda yake a kan tushen farfado da ƙasa, sauyin tattalin arziki da kuma wadata tare.
Ministan ya bayyana tabbacin cewa, tare da haɗin kai da goyon bayan ‘yan Najeriya gaba ɗaya, ƙasar za ta ci gaba da ƙarfafa wajen samun zaman lafiya, ci gaba da bunƙasar tattalin arziki.
A ƙarshe, ya yi fatan alheri ga ‘yan Najeriya a bikin tunawa da ranar samun ‘yancin kai na shekarar 2025, yana masu fatan bikin mai cike da annashuwa da tarihi.
