Trends

CJN Kekere-Ekun Za ta Nada Sababbin SANs 57 a Kotun Koli

Kekere-Ekun babban man shara'ar kotun kolin Nigeriya

Babbar Mai Shari’a ta Najeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, za ta nada sababbin manyan lauyoyi 57 a matsayin Senior Advocate of Nigeria (SAN) a ranar Litinin, 29 ga Satumba, a wani ɓangare na bikin kaddamar da shekarar shari’a ta 2025/2026 na Kotun Koli.

Taron, wanda za a gudanar a babban ɗakin shari’a na Kotun Koli, zai haɗa da zaman musamman da CJN za ta gabatar da jawabi na musamman kan “Halin da Alkalanci ke ciki” (State of the Judiciary).

A cewar sanarwar da Darektan Bayani da Hulɗa da Jama’a na Kotun Koli, Festus Akande, ya fitar, wannan jawabi zai yi nazari kan ayyukan Kotun Koli da tsarin shari’a baki ɗaya a shekarar shari’a ta 2024/2025.

Sanarwar ta ƙara da cewa manyan masu ruwa da tsaki a harkar shari’a za su gabatar da jawabai. Ciki har da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Ƙasa, Shugaban Kungiyar Manyan Lauyoyi (BOSAN), da kuma Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA).

A al’ada, bikin ba kawai na murnar bai wa sababbin lauyoyi wannan gagarumin matsayi na SAN ba ne, har ila yau dama ce ta tunani kan ƙalubale da bukatar gyare-gyare a cikin tsarin shari’a.

Matsayin SAN, wanda ake ɗauka tamkar da taken Queen’s Counsel (QC) a Birtaniya, shi ne mafi girman karramawa da ake bai wa lauyoyi a Najeriya waɗanda suka yi fice wajen gabatar da shari’o’i da kuma bada gudummawa ga ci gaban sana’ar lauya.

Wannan naɗin na farko ne da Mai Shari’a Kekere-Ekun za ta jagoranta tun bayan haurowarta kan mukamin CJN, abin da masana ke ganin ya ƙara ma taron muhimmanci.

Bikin zai fara da ƙarfe 10 na safe, inda za a samu jawabai, tunani da kuma rantsar da sababbin SANs a gaban manyan baki da al’ummar lauyoyi.