Trends

Na fi wahalar Samun Sassaucin Bashi Fiye da Neman Wa’adi na Uku – Obasanjo

Former President of Nigeria Olusegun Obasanjo speaks speaks at the launch of the AU-LED report on Tigray peace process during the 38th African Union (AU) Summit, at the AU Headquarters in Addis Ababa on February 16, 2025. (Photo by Amanuel Sileshi / AFP) (Photo by AMANUEL SILESHI/AFP via Getty Images)

Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya karyata zargin cewa ya taɓa neman ƙara tsawaita wa’adinsa fiye da shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya tanada, yana mai cewa babu wata hujja da ke goyon bayan irin wannan ikirari.

Obasanjo, wanda ya shugabanci Najeriya daga 1999 zuwa 2007, ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba a birnin Accra, yayin taron Democracy Dialogue da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya.

Ya ce maganar cewa ya yi shirin wa’adin mulki na uku ba gaskiya ba ce, yana jaddada cewa babu wani ɗan Najeriya, matacce ko raye, da zai ce ya taɓa kiran sa ya faɗa masa yana da wannan buri.

“Ni ba wawa ba ne. Da na so wa’adin mulki na uku, na san yadda zan bi na samu. Kuma babu wani ɗan Najeriya da zai ce na kira shi na faɗa masa ina so na yi wa’adi na uku,” in ji shi.

Tsohon shugaban ya kuma bayyana cewa ƙoƙarinsa na samun sassaucin bashi ga Najeriya a lokacin mulkinsa ya fi wahalar samu fiye da wani ƙarin wa’adi.

“Ina yawan gaya musu cewa idan na iya samun sassaucin bashi – wanda ya fi wahalar samu fiye da wa’adin mulki na uku – to da ina so wa’adin mulki na uku, da na samu shi ma,” in ji Obasanjo.

Haka zalika, Obasanjo ya yi amfani da dandalin wajen gargadin shugabannin Afirka kan makale da mulki, yana mai cewa shirin zama a kan mulki har tsufa na nuna kuskuren tunanin cewa ba za a iya maye gurbinsu ba.

Ya ce shugabanci yana da kyau a lokacin da shugabanni ke da kuzari da sabuwar hangen nesa, ba lokacin da tsufa ya riske su ba, inda ya jaddada cewa Allah na iya cire kowa a kowane lokaci.

“Wasu ma za su ce ba su da wani da zai gaje su. Ni dai ina ganin hakan zunubi ne ga Allah. Domin idan Allah ya ɗauke ka – wanda zai iya yi a duk lokacin da ya ga dama – wani zai zo ya maye maka guri, kuma wannan sabon shugaban na iya yin abin da ya fi naka kyau ko kuma mara kyau,” in ji shi.