Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025 a matsayin hutu don bikin Maulud, wato ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Sanarwar hakan ta fito ne daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, a madadin Gwamnatin Tarayya. Ya yi murnar taya musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya murnar wannan lokaci mai albarka, tare da kira gare su da su yi koyi da halayen Annabi na zaman lafiya, ƙauna, tawali’u, haƙuri da kuma tausayi.
Dr. Tunji-Ojo ya jaddada cewa waɗannan dabi’un suna da matuƙar muhimmanci wajen gina ƙasa mai ɗorewa, haɗin kai da ci gaban al’umma. Haka kuma, ya roƙi ‘yan Najeriya duk inda suke, ba tare da la’akari da addininsu ba, da su yi addu’a domin samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar nan.
A cewarsa:
“Bikin Maulud na ba mu damar ƙarfafa zumunci, inganta zaman tare cikin lumana, da kuma yin koyi da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) ta girmama juna da hidimar jama’a ba tare da son kai ba.”
Ministan ya ƙara da kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da bin doka, kasancewa masu lura da tsaro, tare da mara wa manufofin gwamnati baya domin cimma haɗin kan ƙasa da cigaban da za a iya dogaro da shi.
Ya kammala da taya musulmi a faɗin Najeriya murnar bikin Mauludi, yana masu fatan shakatawa cikin annashuwa da zaman lafiya.
Sanarwar ta kasance ƙarƙashin sa hannun Dr. Magdalene Ajani, Babban Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

