Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a mayar da Darakta-Janar na Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), Mista Salihu Abdullahi Dembos, da Darakta na Labarai, Mista Ayo Adewuyi, domin su ci gaba da wa’adin aikinsu.
Dembos, wanda aka naɗa a watan Oktoba 2023, ya bar kujerarsa na ɗan lokaci bayan wasu sauye-sauyen shugabanci da aka yi a gidan talabijin na gwamnati. Da wannan umarni na shugaban ƙasa, zai koma ya kammala wa’adin aikinsa na shekaru uku.
Haka kuma, Adewuyi wanda aka naɗa a shekarar 2024, zai koma bakin aiki a matsayin Darakta na Labarai domin kammala wa’adinsa wanda zai kare a shekarar 2027.
Wannan mataki da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya soke sabbin naɗe-naɗen da aka sanar a baya, ciki har da mukaman Darakta-Janar, Darakta na Labarai, Darakta na Tallace-Tallace da kuma Manaja Darakta na NTA Enterprises.
A cewar sanarwar da Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-Tsare, Bayo Onanuga, wannan matakin an ɗauke shi ne domin tabbatar da ci gaba da kuma kwanciyar hankali a shugabancin NTA.

