Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Sufeton ƴan sanda na Najeriya (IGP), Solomon Arase, ya rasu a asibitin Cedarcrest da ke Abuja.
Arase, wanda shi ne IGP na 18 a tarihin Najeriya, an nada shi ne a watan Afrilu, 2015, ta tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
Bayan ya yi ritaya a shekarar 2016, ya ci gaba da bauta wa ƙasa a fannoni daban-daban, musamman matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ƴan sanda (PSC), inda aka nada shi a watan Janairu, 2023, karkashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Sai dai Shugaba Bola Tinubu ya cire shi daga wannan mukamin a watan Yuni, 2024.
Arase, gogaggen jami’in leƙen asiri ne wanda ya taɓa shugabantar Sashen Bincike da Leƙen Asirin Manyan Laifuka, sashen da ya fi girma a harkar leƙen asiri na rundunar ƴan sanda.
Haka kuma ya taɓa zama Kwamishinan ƴan sanda a jihar Akwa Ibom, daga bisani ya zama Mataimakin Sufeto-Janar na ƴan sanda mai kula da harkokin leƙen asiri.
A aikinsa na ƙasa da ƙasa, ya taɓa wakiltar Najeriya a aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Namibia.
A halin yanzu dai, ba iyalan mamacin ko kuma rundunar ƴan sanda ta Najeriya suka fitar da sanarwar tabbatar da wannan lamari ba.
