Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da naɗin Sanusi Mikailu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru, bayan ya samu kuri’u bakwai daga cikin tara da masu zaɓen sarauta suka kaɗa, inda ya doke sauran ‘yan takara guda shida.
Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Abubakar Umar Dutsinmari, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a fadar Sarkin Zuru. Ya ce naɗin ya biyo bayan mika sunayen mutane uku da masu zaɓen sarauta na masarautar Zuru suka gabatar wa Gwamna.
“Daidai da tanadin kundin tsarin mulki da kuma ikon da aka ba shi, Gwamna ya amince da naɗin Alhaji Sanusi Mikail Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru, wanda yanzu aka tabbatar da shi da taken Gomo III,” in ji Dutsinmari.
A lokacin da yake mika takardar tabbatarwa ga sabon sarki, kwamishinan ya bayyana cewa zaben nasa ya ta’allaka ne kan tarihin mutuntaka, bin ka’idojin masarauta da kuma kasancewarsa magajin gadon sarautar.
Ya kuma yi kira ga sabon sarki da ya ci gaba da girmama darajar masarauta tare da kokarin kawo zaman lafiya da ci gaban masarautar Zuru, baya ga tallafawa ayyukan raya ƙasa da Gwamna Idris ke gudanarwa a jihar.
A jawabinsa, sabon Sarkin ya nuna godiya ga Allah Madaukaki da kuma Gwamna Nasir Idris bisa amincewa da shi, inda ya bukaci jama’a da su kasance masu zaman lafiya, biyayya da haɗin kai. Ya yi alkawarin tafiyar da mulki a bude tare da bai wa kowa dama.
Sarkin ya kuma yi godiya ga Chief na Wasagu, wanda ya yi aikin rikon sarki a lokacin mulkin naɗewa, bisa jagoranci nagari da ya nuna, tare da sha alwashin ci gaba da tallafawa al’ummar masarautar kamar yadda ya saba.
