Trends

Dole mu Gudanar da Gangami Taron Jam’iyya – Gwamnonin PDP

Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) sun fito daga taronsu a Gusau, babban birnin jihar Zamfara a ranar Asabar, inda suka jaddada aniyar su na ci gaba da gudanar da babban taron zaɓe na kasa da aka shirya a Ibadan, jihar Oyo, ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Wannan matsayi na gwamnonin ya zo ne a yayin da tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa bai san da taron ba kuma bai amince da zaman kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ya yanke hukuncin shirya taron ba.

Wike ya kuma ce ba za a samu zaman lafiya a jam’iyyar ba, sai an amince da sakamakon taron fidda gwanin yankin Kudu maso Kudu da magoya bayansa suka gudanar wanda ya haifar da fitar Dan Orbih amma kwamitin gudanarwa na jam’iyya ya yi watsi da shi.

Sai dai gwamnonin PDP sun nuna goyon bayan su ga shugabancin riko na Ambassador Umar Damagum, inda suka tabbatar da biyayya ga kudurorin zaman NEC na 101 da aka gudanar a watan Yulin 2025 game da babban taron jam’iyyar.

“Forum ɗin na tabbatar da cikakken goyon bayansa ga kudurorin zaman NEC na 101, musamman game da taron kasa na Nuwamba 15. Muna kira ga mambobi su guji duk wani yunƙuri na janye taron daga hanyar da aka tsara, domin PDP ita ce kadai cibiyar dimokuraɗiyya kuma zabin da ya dace domin mayar da Najeriya kan tafarkin kyakkyawan mulki da cigaban ƙasa.”

Gwamnonin sun kuma gode wa mambobi da magoya bayan PDP bisa jajircewar su da goyon baya “duk da tsananin tsoratarwa da kuma matakan adawa da dimokuraɗiyya daga gwamnatin APC a yayin zaɓen cike gurbi da ya gabata.”

Forum ɗin ya yaba da jajircewar shugabannin PDP da mambobi wajen shawo kan kulle-kullen ficewar mambobi daga jam’iyya, inda suka ce irin waɗannan shashanci ba za su rage tasirin jam’iyyar a ƙasa ba ko kuma burin jama’a na ganin an dawo da sauƙin rayuwa da tsaron da aka shaida a lokutan mulkin PDP.

Sun kuma shawarci mambobi da magoya bayan jam’iyyar da ‘yan Najeriya gaba ɗaya da su ci gaba da rungumar hangen nesa da ka’idojin PDP duk da matsin lamba daga gwamnatin APC, suna mai cewa:

“Wannan hali na nuna azalzala ya nuna cewa jam’iyyar da ke mulki ba ta da tsari, ba ta da hangen nesa, kuma a ƙarshe dole ne ta fuskanci ƙin amincewa daga talakawa.”

Game da zaɓen cike gurbi na ranar 9 ga watan Agusta, gwamnonin PDP sun yi Allah-wadai da “yadda aka mamaye zaɓen da sojoji, inda aka samu maguɗi sosai, sayen ƙuri’u da tashin hankali.” Sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su fi taka-tsantsan wajen kare ƙuriyoyinsu.

A batun tsaro, Forum ɗin ya yaba da matakan da gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauka wajen rage matsalar tsaro a jihar, amma sun nuna damuwa kan “ci gaba da kisan gilla a jihohin Katsina, Filato, Neja da Benue da sauran sassan ƙasar.” Sun bukaci gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.