Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar a Jihar Kano.
A yayin bayyana sakamakon ranar Lahadi, Jami’in Zaɓe mai dawo da sakamako, Farfesa Muhammad Waziri daga Jami’ar Bayero Kano, ya bayyana dan takarar APC, Garba Gwarmai, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 31,472.
Ya doke dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Yusuf Maigado, wanda ya samu kuri’u 27,931.
Zaɓen na cike gurbi an gudanar da shi ne bayan an ayyana sakamakon zaɓen farko da aka yi a mazabar a matsayin wanda bai kammalu ba.
Da tazara ta kuri’u 3,541, wannan nasara ta Garba Gwarmai ta kara ƙarfafa tasirin jam’iyyar APC a fadin jihar.



