Farashin Kaya: Rahoton NBS Ya Nuna Hauhawan Ta Sauka zuwa Kashi 21.8%

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa adadin hauhawar farashin kaya a Najeriya ya sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni.

NBS ta sanar da hakan ne a cikin rahoton Consumer Price Index (CPI) da ta fitar a ranar Juma’a, wanda ya nuna wannan shi ne karo na hudu a shekarar 2025 da aka samu raguwar hauhawar farashin kaya (disinflation).

A cewar hukumar:

“A watan Yuli 2025, adadin hauhawar farashin kaya ya ragu da kashi 0.34% idan aka kwatanta da na watan Yuni 2025.”

Rahoton ya nuna cewa, idan aka kwatanta shekara da shekara, adadin da aka samu a watan Yuli 2025 ya yi ƙasa da na watan Yuli 2024 (33.40%) da kashi 11.52%.

Sai dai, idan aka duba wata zuwa wata (month-on-month), adadin a watan Yuli 2025 ya kai 1.99%, wanda ya fi na watan Yuni 2025 (1.68%) da kashi 0.31%. Wannan na nufin cewa a watan Yuli, saurin ƙaruwa a farashin kaya ya fi na watan da ya gabata.

NBS ta ce manyan sassan tattalin arziki da suka fi haifar da hauhawar farashin kaya sun haɗa da:

Abinci da abin sha marar giya

Ayyukan gidaje da masauki

Sufuri

Rahoton ya kuma nuna cewa hauhawar farashin abinci (food inflation) a watan Yuli 2025 ya kai 22.74% idan aka kwatanta shekara da shekara, wanda ya tashi daga 21.97% a watan Yuni 2025. Wannan adadi ya yi ƙasa da na watan Yuli 2024 (39.53%) da kashi 16.79%.

Hukumar ta ce babban dalilin wannan raguwar hauhawar farashin abinci na shekara-shekara shi ne sauya shekarar ma’auni (base year).

Idan aka duba wata zuwa wata, hauhawar farashin abinci a watan Yuli 2025 ya kai 3.12%, wanda ya ragu da kashi 0.14% idan aka kwatanta da watan Yuni 2025 (3.25%). Wannan raguwar ta samo asali ne daga saukar farashin:

Man gyada

Wake fari

Shinkafa ta gida

Garin masara

Dawa

Garin alkama

Gero danye, da sauransu.

Rahoton ya ƙara bayyana cewa matsakaicin hauhawar farashin abinci na shekara guda daga watan Yuli 2024 zuwa Yuli 2025 ya kai 26.97%, wanda ya yi ƙasa da na shekarar da ta gabata (36.36%) da kashi 9.39%.