Tsohon dan wasan Arsenal, Thomas Partey, ya samu beli na wucin-gadi bayan gurfana a gaban kotu a birnin Landan ranar Talata domin fuskantar tuhuma kan laifin fyade da cin zarafin jima’i.
Dan wasan kasar Ghana mai shekaru 32 yana fuskantar tuhumar fyade sau biyar da aka ce ya aikata wa mata biyu, da kuma tuhuma guda kan cin zarafi na jima’i da aka ce ya yi wa wata mata ta uku.
An ce laifukan sun faru ne tsakanin shekarar 2021 da 2022 lokacin da yake wasa a kungiyar Arsenal. An gurfanar da Partey ne a ranar 4 ga Yuli, bayan kwangilarsa da Arsenal ta kare a karshen watan Yuni.
Yayin da ya bayyana a kotun Westminster Magistrates, Partey ya tsaya a akwatin masu laifi sanye da rigar riga bakar fata tare da sanya hannuwansa a bayansa. Bai nuna wata alama ba yayin da ake karanta tuhumar, kuma ba a bukaci ya amsa tuhumar ba. Lauyarsa, Jenny Wiltshire, ta taba bayyana a baya cewa Partey “yana musanta dukkan tuhumomin da ake masa” kuma “yana maraba da damar kare sunansa.”
A cikin sharuddan belinsa, an haramta masa yin wata hulɗa da kowanne daga cikin matan uku da ake magana a kansu, sannan dole ne ya sanar da ‘yan sanda duk lokacin da zai canza matsuguninsa ko kuma ya yi shirin tafiya kasashen waje.
Yayin da ake tattaunawa kan sharuddan beli, Babban Alkali Paul Goldspring ya ce, “Na fahimci ba ya aiki a wannan ƙasar yanzu kuma yana wasa a ƙasar Sifaniya,” yana nuni da rahotannin da ke cewa Partey yana shirin komawa kungiyar Villarreal da ke Sifaniya.
Za a ci gaba da sauraron shari’ar Partey a babbar kotun Old Bailey da ke birnin Landan a ranar 2 ga Satumba.
Wani kakakin kungiyar Arsenal Supporters Against Sexual Violence ya bayyana “matukar bakin ciki” da yadda kulob din Arsenal ya tafiyar da lamarin.
Honor Barber ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na PA cewa, “Ba mu taba son kasancewa a cikin wannan hali ba, inda kulob din da muke so, da kuma darajojin da muke goyon baya, ke buga wasa da dan wasa da ke fuskantar shari’a kan laifukan fyade guda shida.”
KARANTA HAKA MA: UEFA ta haramta FK Arsenal Tivat shiga gasanni na tsawon shekaru 10 saboda zamba a wasa
Barber ta ce kungiyar ta gudanar da zanga-zanga “a wajen kusan dukkanin wasannin gida a bara domin karya shiru da kulob din ke yi kan wannan batu.” Ta kara da cewa suna bukatar kulob din ya fitar da manufofinsa kan batun cin zarafi na jima’i, “ya dakatar da duk dan wasa da ake bincika kan laifukan jima’i,” kuma “ya bayar da cikakken tallafi ga wadanda abin ya shafa.”
Rundunar ‘yan sandan Birtaniya ta tabbatar da cewa sun fara samun rahoton da ya shafi fyade a watan Fabrairun 2022.
Partey ya koma Arsenal daga Atletico Madrid



