Trends

D’Tigress Ta Lashe Kofin Afrobasket Na Mata Karo Na Biyar a Jere

Yan wasan D’Tigress da suka lashe Kofin AfroBasket Ball

Kungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, ta kafa tarihi a ranar Lahadi bayan da ta zama kungiya ta farko da ta lashe gasar FIBA Women’s AfroBasket har sau biyar a jere, bayan doke kasar Mali a wasan karshe.

Tun a ranar Asabar, D’Tigress ta samu gurbin shiga wasan karshe bayan da ta doke kasar Senegal da ci 75-68 a wasan kusa da karshe na gasar da aka gudanar a shekarar 2025.

Wannan nasara ta tabbatar da D’Tigress a matsayin babbar cibiyar kwallon kwando ta mata a nahiyar Afrika, kuma ta kara daukaka sunan Najeriya a fagen wasanni.

Karin bayani na tafe…