Hatsarin Mota: NUJ FCT Council ta yi Jimamin Mutuwar ’Yan Jarida Bakwai Daga Gombe
Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Babban Birnin Tarayya (FCT), ta bayyana alhini mai zurfi kan mutuwar ’yan jarida daga Jihar Gombe da suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota. Shugabar NUJ FCT Council, Comrade Grace Ike, a cikin sakon ta’aziyya da ta aikawa Shugaban NUJ na ƙasa, Comrade Alhassan Yahya, da mambobin…










