Gombe 2027: PDP ta Bai wa Pantami Takardar Takara
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bai wa Farfesa Isa Ali Pantami, CON, Takardar Tabbatar da Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Gombe, wanda ke tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2027. An gudanar da bikin miƙa takardar ne a ranar Laraba yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar…
