Wani Dan Shekara 70 Ya Kashe Kanwar sa Kan Rabon Gado a Jigawa
Rundunar yansandan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan gado. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yansandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi a yankin ƙaramar hukumar Dutse –…
