Wani sabon rahoton masana’antu ya bayyana cewa motocin asibiti na gwamnati a Najeriya na daukar kashi 7% kacal na lamurran gaggawa na lafiya, duk da fadada Shirin Kasa na Ayyukan Gaggawa da Motocin Asibiti (NEMSAS) zuwa jihohi 30.
Rahoton gaggawa na Salvus na zangon farko na shekarar 2026 (Q1 2026), wanda Emmanuel Oziwa-John ya wallafa, ya nuna cewa yawancin ‘yan Najeriya na dogaro ne da hanyoyi na kashin kai ko na gargajiya wajen kai marasa lafiya lokacin gaggawa.
Motocin haya (kamar bas-bas na kasuwanci) na daukar kashi 47% na masu bukatar kulawar gaggawa, yayin da kashi 31% ke zuwa asibiti ta motocin kansu ko kuma su rika tafiya da kafa. Motocin asibiti masu zaman kansu kuwa na daukar kusan kashi 15% na irin wadannan lamurra.
A cewar rahoton, Najeriya na fuskantar sama da lamurran gaggawa miliyan shida a duk shekara, amma har yanzu yaduwar NEMSAS bai wuce kashi 0.2% ba.
Mutane da dama na kauce wa amfani da motocin asibiti saboda tsoron biyan kudi a gaba, duk da cewa gwamnati ta tabbatar da ba da kulawar gaggawa kyauta na awanni 48 na farko.
Rahoton ya ce, “Tsarin na gazawa ne ba saboda rashin kayan aiki ba, amma saboda rashin daidaito a hadin kai, hanyoyin tura marasa lafiya, da kuma yadda ake mika su daga wuri zuwa wuri. Matsalar tana cikin tsarin hada kai gaba daya.”
Haka kuma, lokutan amsa kira na gaggawa na da jinkiri. A jihar Legas, ana daukar kimanin mintuna 17 kafin isa wurin gaggawa, wanda ya ninka fiye da ka’idar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta mintuna takwas. A yankunan karkara kuwa, jin ƙirin na iya wuce awa biyu.
Rahoton ya kiyasta cewa tsakanin kashi 10 zuwa 15 cikin dari na mutuwar mutane miliyan 1.6 a shekara a Najeriya na faruwa ne a sassan kula da gaggawa a asibitoci, galibi saboda marasa lafiya na zuwa a makare ko kuma ba tare da samun kulawar farko kafin isa asibiti ba.
Sauran matsalolin da aka gano sun hada da rashin musayar bayanai yadda ya kamata, karancin shirin karbar marasa lafiya a asibitoci, jinkirin samun kudade, karancin masu inshorar lafiya, da kuma rashin rajistar kwararrun ma’aikatan gaggawa (paramedics) a matakin kasa.
Rahoton ya kuma nuna cewa kashi 55% kacal na wadanda NEMSAS ta dauka a zangon uku na shekarar 2025 aka kai su asibitocin da ke da ingantattun sassan kula da marasa lafiya masu tsanani (ICU) ko kuma sassan gaggawa masu iya kula da rauni mai tsanani.
A karshe, rahoton ya bayyana cewa kalubalen kula da lafiyar gaggawa a Najeriya ba zai warware ta hanyar kara yawan motocin asibiti kadai ba, sai an inganta hadin kai, gina amincewa da jama’a, inganta tsarin aika agaji, da kuma hada bayanai a ainihin lokaci a fadin bangaren lafiya.
