El-Rufai ya ci Gaba da Kare Kan sa a Kotu Bayan Jana’izar Mahaifiyar sa

Nasir El-Rufai Tsohon Gwamnan Kaduna

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya koma Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar Talata domin sauraron bukatar belinsa a shari’ar zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa.

An kawo El-Rufai kotu ne karkashin tsauraran matakan tsaro, irin wanda ya kasance a lokacin da aka gurfanar da shi a makon da ya gabata.

A makon jiya ne aka gurfanar da shi a gaban Mai shari’a Rilwan M. Aikawa bisa tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati, mallakarsu ba bisa ka’ida ba, da kuma safarar kudaden haram (money laundering).

An gabatar da tsohon gwamnan a kotu ne bayan shafe sama da wata guda a tsare, lamarin da ya jawo hankalin jama’a matuka kan wannan shari’a mai daukar hankali.

Bayan gurfanar da shi, kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga Maris, 2026, domin sauraron bukatun da ke gaban kotu, ciki har da neman belinsa.

Sai dai a ranar 27 ga Maris, 2026, Hukumar Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) ta sake shi na wucin gadi bisa dalilan jin kai, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Ummar El-Rufai, a birnin Alkahira na kasar Masar.

A wani sabon salo a shari’ar, an kuma gurfanar da El-Rufai tun da fari a ranar Talata a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Kawo kan wasu tuhume-tuhume daban.

A kotun jihar, an gurfanar da shi tare da wani Amadu Sule bisa zargin cin zarafin mukami, damfara, yunkurin aikata damfara, da kuma ba da gata ba bisa ka’ida ba.

Wadannan tuhume-tuhume, duk da cewa ICPC ce ta shigar da su, sun bambanta da wadanda ke gaban Babbar Kotun Tarayya.

Bayan kammala shari’ar a kotun jihar, hukumar ta mayar da El-Rufai zuwa Babbar Kotun Tarayya da ke cikin harabar kotun a Kaduna.

A halin yanzu, ana ci gaba da sauraron shari’ar a Babbar Kotun Tarayya, inda bukatar belinsa ke kan gaba.

Masu lura da harkokin shari’a sun ce sakamakon hukuncin belin na iya tasiri ga mataki na gaba na shari’ar, la’akari da girman zarge-zargen da ake masa.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana ci gaba da gabatar da hujjoji kan bukatar belin, inda ake sa ran kotu za ta yanke hukunci daga baya a ranar ko kuma a wani lokaci na gaba da za a sanar.