Gawuna Ya Fice Daga APC, ‘Zai Gana da Kwankwaso’

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kano a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a hukumance.

A cikin wata takardar murabus da ya rubuta ranar 29 ga Maris, 2026, wadda ya aika wa shugaban APC na mazabar Gawuna a Karamar Hukumar Nassarawa, Gawuna ya bayyana matakin nasa a matsayin “na kansa kuma na son rai.”

Ya ce, “Ina sanar da ficewata daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance, daga ranar 29 ga Maris, 2026.”

Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta.
Sai dai bai bayyana matakin siyasa na gaba da zai dauka ba.

Ficewar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano, inda manyan ‘yan siyasa ke canza sheka da kulla sabbin kawance gabanin zabuka masu zuwa.

Majiyoyi na kusa da tsohon mataimakin gwamnan sun bayyana cewa ana sa ran zai gana da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Ana kallon wannan ci gaban a matsayin wani bangare na dabarun siyasa da ke kara zafi a jihar, musamman bayan wasu sauye-sauye da hadin gwiwa tsakanin manyan jiga-jigan siyasa.