FG Ta Yi Gargadin Karancin Kwararrun Ma’aikatan Lafiya na Musamman

Ministan Ilimi Dr. Tunji Alausa

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar matsanancin karancin kwararrun ma’aikatan lafiya na musamman, musamman a fannoni kamar Occupational Therapy, Audiology da Speech Therapy, a cewar Ministan Ilimi, Tunji Alausa.

A jawabin da ya gabatar a yayin kaddamar da Kwamitin Kasa na bunkasa ilimin Occupational Therapy, Audiology da Speech Therapy a Abuja, Alausa ya ce wannan gibi na iya kawo cikas ga samar da ingantaccen kiwon lafiya, hadin kai a cikin al’umma, da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa.

Ya ce, “Muna a wani lokaci mai muhimmanci a ci gaban kasarmu, inda bukatar kwararrun ayyukan kiwon lafiya da gyaran jiki ke karuwa cikin sauri,” yana mai jaddada cewa asibitoci, makarantu da al’umma na bukatar kwararrun ma’aikata cikin gaggawa.

Ministan ya bayyana cewa har yanzu jami’o’in Najeriya ba su samar da tsararrun shirye-shiryen digiri a wadannan fannoni ba, yayin da horon da ake da shi yake da karanci ko kuma bai dace da ka’idojin duniya ba.

Ya kara da cewa, “Wannan gibi na da tasiri ga yadda ake ba da sabis, bunkasar ma’aikata, da kuma ikonmu na cimma ka’idojin kasa da na duniya.”

Alausa ya ce Gwamnatin Tarayya na aiki tare da National Universities Commission (NUC) da kuma Tertiary Education Trust Fund (TETFund) domin fadada shirye-shiryen karatu, inganta ingancin ilimi, da kuma samar da dalibai masu gogayya a duniya.

Shugabar kwamitin, Victoria Amu, ta yi alkawarin magance gibin horo da karancin ma’aikata. Ta ce, “Karfafa ilimi a wadannan fannoni zai inganta ayyukan kiwon lafiya, kara saurin gano cututtuka da fara magani da wuri, tare da taimakawa mutane su rayu cikin inganci.”

Ta kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki—ciki har da jami’o’i, kungiyoyin kwararru da kamfanoni masu zaman kansu—da su bada gudunmawa, tana mai cewa hadin kai ne zai tabbatar da dorewar wannan shiri.

Kididdiga ta nuna tsananin karancin kwararru a Najeriya: zuwa shekarar 2024, akwai kwararrun Occupational Therapy guda 163 kacal, Speech Therapy da Audiology guda 103, da kuma prosthetists da orthotists guda 200—adadi mai matukar kasa idan aka kwatanta da yawan jama’ar kasar da ya haura miliyan 200.