Rage Tallafi Na Barazana ga Tsaron Lafiyar Najeriya – Rahoto

A USAID flag flutters outside, as the USAID building sits closed to employees after a memo was issued advising agency personnel to work remotely, in Washington, D.C., U.S., February 3, 2025. REUTERS/Kent Nishimura

Ikon Najeriya na gano da kuma daukar mataki kan barkewar cututtuka na fuskantar barazana sakamakon tangardar kudade da ke raunana tsarin sa ido, dakunan gwaje-gwaje, da hanyoyin jigilar samfurori, a cewar wani sabon rahoto da Resolve to Save Lives (RTSL) ta fitar.

Rahoton mai taken “A System in Transition: Nigeria Country Report”, wanda aka gabatar a Abuja, ya yi gargadin cewa raguwar tallafin masu bayar da gudunmawa da gibi a kudaden cikin gida na sanya muhimman tsare-tsaren tsaron lafiya cikin hadari.

Daraktar RTSL a Najeriya, Nanlop Ogbureke, ta ce wannan rahoto ya zo ne a wani lokaci mai muhimmanci ga bangaren lafiya na kasar.

Ta ce, “Lokacin da kudade suka sauya, matsaloli na kara bayyana,” inda ta jaddada cewa matakan da za a dauka yanzu za su tantance ko Najeriya za ta karfafa tsarin lafiyarta ko kuma ya rabu-rabu.

Najeriya ta dade tana amfana da tallafin kasashen waje, musamman daga USAID, wanda ya taimaka wajen karfafa yaki da HIV, kula da lafiyar mata masu juna biyu, da kuma tsarin sa ido kan cututtuka.

Sai dai dakatar da wasu shirye-shiryen USAID a baya-bayan nan ya bayyana raunanan bangarori, musamman a dakunan gwaje-gwaje, kwanciyar hankalin ma’aikata, da kuma shirye-shiryen tunkarar annoba.

Rahoton ya nuna wasu matsaloli kamar tsarin sa ido na dijital da ke tafiya a layi daban-daban da kuma dakunan gwaje-gwaje na cututtuka daban-daban, wanda ke kara kashe kudi ba tare da inganta sakamako ba.

Ya kuma bayyana cewa Najeriya na da ginshikan da za su ba ta juriya, amma tana fama da rashin hadin kai da daidaituwa. Ogbureke ta ce, “Kalubalen ba rashin kwarewa ba ne, illa rashin daidaito, hadin kai da kuma aiki tare.”

Jami’an jihohi sun tabbatar da tasirin hakan. Kwararren likitan sa ido kan cututtuka na Jihar Kaduna, Jeremiah Daiko, ya ce raguwar tallafi na nufin dole Najeriya ta dogara da kanta wajen tallafawa sa ido, dakunan gwaje-gwaje da kuma martanin barkewar cututtuka.

Haka kuma, Daraktan CDC na Jihar Kano, Muhammad Abbas, ya yi gargadin cewa hukumomin jihohi na cikin hadari, yana mai kira ga jihohi da su samar da hanyoyin da za su dore da kansu.

Kwararriyar harkokin kudade ta jama’a, Udeme Edumoh, ta bayyana raguwar tallafin kasashen waje a matsayin “alheri,” domin yana tilasta Najeriya ta gyara kura-kurai tare da barin tsarin kula da cuta daya bayan daya zuwa tsarin hadin gwiwa.

Ta ce, “Dole mu duba abin da kudadenmu ke haifarwa, ba wai abin da ake kashewa kadai ba.”

Rahoton ya kuma nuna damar yin gyare-gyare, ciki har da hade tsarin sa ido da kayan aiki, tabbatar da kwanciyar hankalin ma’aikatan lafiya, da kuma karfafa cibiyoyin gudanar da ayyukan gaggawa.

Ogbureke ta kammala da cewa, “Ba za mu ci gaba da dogaro da wasu wajen kula da lafiyarmu ba. Dorewa dole ta kasance a tsakiyar duk abin da muke yi.”