Taron APC: Gwamnatin Tarayya ta Rufe Hanyoyi Zuwa Eagle Square

Gwamnatin Tarayya ta sanar da rufe dukkan hanyoyin shiga da fita da ke kewaye da Federal Secretariat Complex da Eagle Square daga ranar Juma’a, 27 ga Maris zuwa Asabar, 28 ga Maris, 2026, gabanin babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A cikin wata takarda da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya fitar a ranar Alhamis, an umurci dukkan Ma’aikatu, Sassa da Hukumomi (MDAs) da ke cikin matakai na I, II da III na Federal Secretariat Complex, da kuma Ma’aikatar Harkokin Waje, da su lura da wannan ci gaba.

Takardar, wadda Dr. Abdul S. U. Garba, Babban Sakatare a Sashen Jin Dadin Ma’aikata ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa rufe hanyoyin ya zama dole ne saboda za a yi amfani da Eagle Square a matsayin wurin gudanar da taron jam’iyyar mai mulki.

“Sakamakon haka, dukkan ma’aikatan da ofisoshinsu ke cikin wuraren da abin ya shafa su yi aiki daga gida a ranar Juma’a, 27 ga Maris, 2026,” in ji takardar.

Haka kuma, an umurci manyan sakatarori da shugabannin hukumomi da su tabbatar da cewa an yada wannan bayani ga dukkan ma’aikata tare da tabbatar da cikakken bin umarnin.

Federal Secretariat Complex, wanda ke kan titin Shehu Shagari Way a yankin Three Arms Zone na Abuja, na dauke da muhimman ofisoshin gwamnati, kuma yawanci yana fuskantar cunkoson ababen hawa, wanda ake sa ran zai kara dagulewa a cikin kwanakin biyu na rufe hanyoyin.