Trends

Fitowar Hakora Ba Ta Haifar da Gudawa ga Jarirai — Kwararru

Kwararrun lafiyar hakora a Ibadan sun karyata rade-radin da ake yi cewa fitowar hakora na haifar da gudawa ga jarirai, inda suka bayyana cewa yawan yin bayan gida yana faruwa ne saboda yara na rarrafe a wurare masu datti tare da saka abubuwa a baki.

Sun bayyana hakan ne yayin bikin World Oral Health Day (WOHD), mai taken “A Happy Mouth is a Happy Life”, inda suka gargadi iyaye da su guji amfani da hanyoyi masu hadari kamar shafa man inji ko ruwan batir don maganin matsalolin hakora, saboda hakan na iya jawo konewar sinadarai da guba.

Daya daga cikin kwararrun, Folake Lawal daga University College Hospital (UCH), ta bayyana cewa fitowar hakora na iya haifar da dan radadi ko rashin natsuwa da kuma yawan taba baki, amma zazzabi mai tsanani ko wasu alamomi masu tsauri na bukatar ganin likita. Ta bukaci iyaye su nemi kulawar kwararru a kan lokaci.

Ta kuma jaddada cewa samun damar kula da lafiyar baki a Najeriya yana da karanci, inda adadin likitocin hakora bai kai yadda World Health Organization (WHO) ta tsara ba. Ta kara da cewa cin abinci mai yawan sukari na haddasa rubewar hakora, kiba da kuma cutar sikari.

Wata kwararriya a UCH, Aderonke Dedeke, ta gargadi jama’a da su guji amfani da burushin hakora mai kauri sosai, da kuma dabi’u masu hadari kamar goge hakora da reza. Ta bukaci a hada kula da lafiyar baki cikin tsarin kula da lafiya na farko, tare da aiwatar da manufofin lafiyar baki na kasa.

Shi ma Farfesa Olushola Ibiyemi na University of Ibadan ya nuna damuwa kan karuwar cututtukan hakora kamar rubewar hakori (dental caries), kumburin danko (gingivitis), cutar danko mai tsanani (periodontitis), da kuma cutar kansar baki. Ya danganta hakan da rashin tsafta da kuma yawan cin sukari. Ya bukaci jama’a su rika duba hakoransu a kalla sau daya a shekara tare da wayar da kai a al’umma.

Kwararrun sun kuma bayyana cewa rashin kula da tsaftar baki a lokacin daukar ciki na iya haifar da haihuwar jarirai masu karancin nauyi, yayin da shan taba da miyagun kwayoyi ke kara hadarin kamuwa da cutar kansa a baki, makogwaro da huhu.

Sun yi kira da a kara zage damtse wajen wayar da kai kan lafiyar baki, ilimantarwa da kai dauki ga al’ummomin da ba su da kulawa sosai, tare da gargadin cewa rade-radi da hanyoyi masu hadari na ci gaba da jefa lafiyar yara cikin hadari.
MAJIYA: People’s Gazette