Trends

Kudin Kati: FAAN Ta Fara Sabon Tsari na Biyan Kuɗi

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta sanar da fara aiwatar da tsarin biyan kuɗi ba da tsabar kuɗi ba (cashless) a dukkan filayen jiragen sama na ƙasar, daga ranar 1 ga Maris, 2026.

Manajan Darakta ta FAAN, Olubunmi Kuku, ta ce matakin na da nufin dakile zubewar kuɗaɗen shiga tare da ƙarfafa gaskiya da ɗaukar alhaki.

“Wannan shiri yana da alaƙa da gaskiya da dorewa. Muna tabbatar da cewa duk wata kobo da ta dace da Gwamnatin Tarayya an tattara ta ba tare da zubewa ba,” in ji ta ga manema labarai bayan bayyanarta a gaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Wakilai.

Sabon umarnin ya shafi biyan kuɗaɗe a ƙofofin shiga filin jirgi, wuraren ajiye motoci, da ɗakunan VIP, inda aka wajabta wa fasinjoji amfani da hanyoyin dijital maimakon tsabar kuɗi.

FAAN ta bayyana cewa ta tara Naira biliyan 387.8 a shekarar 2024 da kuma Naira biliyan 483.1 a 2025, tare da samun sama da kashi 88 cikin ɗari na yawan tattarawa. An kuma cire wasu kuɗaɗe kai tsaye zuwa Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na Gwamnatin Tarayya (Consolidated Revenue Fund), yayin da sauran suka rage domin kashe kuɗin gudanarwa da ayyukan ci gaba.

Kwamitin Kuɗi na Majalisar Wakilai, ƙarƙashin jagorancin James Faleke, ya umurci FAAN da ta gabatar da takardun bayanai da ke goyon bayan yawan kuɗaɗen shiga da aka tara da kuma kuɗaɗen da aka mayar domin ƙarin nazari.

An fara aiwatar da tsarin cashless mai taken “Operation Go Cashless” tun a watan Satumbar 2025 a filin jirgin sama na MMIA da ke Legas da kuma NAIA da ke Abuja, saboda yawan zirga-zirgar da suke da shi. FAAN ta haɗa kai da kamfanin Paystack domin girka na’urorin karɓar kuɗi ba tare da taɓa kuɗi ba a wuraren tattara kuɗaɗen shiga.

Duk da cewa FAAN ta ce tsarin zai inganta harkokin filayen jiragen sama tare da rage zubewar kuɗaɗe, wasu fasinjoji sun koka kan cinkoso da rasa jirage yayin aiwatar da tsarin, lamarin da ya haifar da damuwa kan saurin aiwatarwa.

Sai dai hukumar ta ba matafiya tabbacin cewa za a samar da wuraren ba da bayanai da kuma shafinta na yanar gizo domin ba da jagora, tana kuma kira ga ‘yan Najeriya da su tanadi hanyoyin biyan kuɗi na dijital kafin su isa filayen jiragen sama.