Trends

Ƙarami Minista: Tinubu Ya Naɗa Taiwo Oyedele a Matsayin Ministan Kuɗi

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Taiwo Oyedele a matsayin Ministan Kuɗi na Ƙasa (Ƙarami), inda zai maye gurbin Dokta Doris Uzoka-Anite.

Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Onanuga ya kuma ce Uzoka-Anite za ta koma Ma’aikatar Tsare-Tsaren Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Ƙasa a matsayin Ministar Ƙasa (Ƙarami), wanda hakan ya zama mukami na uku da take riƙewa a wannan gwamnati.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya aike da sunan Oyedele zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa, ta wata wasiƙa da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Kafin wannan naɗi, Oyedele, ɗan asalin Ikaram, Akoko a Jihar Ondo, shi ne shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Haraji da Gyaran Tsarin Haraji, wanda ya jagoranci sauye-sauye a tsarin harajin Nijeriya.

Oyedele mai shekaru 50 masanin tattalin arziƙi ne, ƙwararren akawu kuma masani a fannin manufofin gwamnati. Ya yi karatu a Kwalejin Fasaha ta Yaba (Yaba College of Technology), inda ya samu Babbar Difloma ta Ƙasa (HND) a fannin lissafin kuɗi da harkokin kuɗi. Daga bisani ya samu digirin farko (BSc) a fannin lissafin kuɗi na aikace (Applied Accounting) daga Jami’ar Oxford Brookes.

Haka kuma ya halarci shirye-shiryen ƙarin horo na shugabanci a London School of Economics, Jami’ar Yale, Gordon Institute of Business Science, da Harvard Kennedy School.

Oyedele ya kwashe shekaru 22 yana aiki a kamfanin PwC, inda ya shiga a shekarar 2001, kuma ya kai matsayin Abokin Hulɗa kan Manufofin Kuɗi da Jagoran Haraji na Afirka.

Bugu da ƙari, shi farfesa ne a Jami’ar Babcock da ke Jihar Ogun, sannan malami ne mai ziyara a Lagos Business School.