Kungiyar ‘Yan Kasuwar Mai Masu Zaman Kansu ta Najeriya, Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN), na shirin neman rancen kudi domin gina matatar mai ta dala biliyan 10.
Matakin ya biyo bayan sauye-sauyen farashi da ake samu daga manyan masu samar da mai a kasuwa, ciki har da Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals (DPRP).
A bana, matatar mai mai karfin tace ganga 650,000 a rana ta sauya farashi sau uku, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa cikin yanayin riba da asara. Duk da cewa sauyin farashin danyen mai – wanda shi ne babban ginshikin farashin – na da tasiri, rashin tabbas din ya jefa ‘yan kasuwar cikin fargaba da daukar asarar sauyin kasuwa.
Da yake zantawa ta wayar tarho, Shugaban IPMAN na kasa, Alhaji Abubakar Maigandi, ya ce mafita mafi sauki ga wannan matsala ita ce kungiyar ta gina tare da sarrafa nata matatar mai a cikin kasar nan.
Ya bayyana karancin kudade a matsayin babban kalubalen da ke hana fara aikin matatar mai mai karfin ganga 300,000 a rana.
A cewarsa, wurin da aka ware domin aikin, mai suna IPMAN Refinery and Petrochemicals Company, yana Jihar Akwa Ibom.
Maigandi ya kara da cewa kungiyar za ta gabatar da shirin da bukatar rancen kudin ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Maris.
Ya ce da zarar an samu rancen, wanda ka iya hada da jarin hadin gwiwa (equity), za a iya kammala aikin cikin shekara guda.
Da aka tambaye shi ko ‘yan kasuwar za su ci gaba da dogaro da Dangote har abada, Maigandi ya ce: “’Yan kasuwa masu zaman kansu za su nemi goyon bayan gwamnati domin gina tasu matatar mai.
“Mun kammala shirye-shiryenmu, kuma za mu gabatar da su ga Shugaban kasa a watan Maris.
“Matatar mai mai suna IPMAN Refinery and Petrochemicals Company tana Jihar Akwa Ibom, kuma tana da karfin ganga 300,000 a rana. Za ta ci kudin dala biliyan 10, kuma za mu kammala ta cikin shekara guda.”
Tun bayan da Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ta daina zama ita kadai mai shigo da kuma rarraba man fetur bayan cire tallafin mai, matatun gwamnati na Fatakwal da Warri sun daina aiki.
Baya ga DPRP, wanda bayanan Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) suka nuna yana samar da lita miliyan 40.1 daga cikin lita miliyan 63 na bukatar cikin gida, ragowar lita miliyan 23 ana shigo da su ne daga kasashen waje, saboda kananan matatun cikin gida ba su da karfin tace fetur (PMS) yadda ya kamata.
Shugaban IPMAN ya kuma bayyana cewa ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun fara karbar man fetur daga Dangote.
Sai dai ya ce tun da matatar ba ta fara kai musu fetur kai tsaye ba kamar yadda aka yi alkawari, suna karbar man ne ta hannun kamfanin MRS Oil Nigeria Plc.
A cewarsa, tunda har yanzu suna kashe kudi wajen jigilar man daga MRS zuwa gidajen mai nasu, ba za su iya sayar da shi a farashi daya da MRS ba.
“Ba za mu iya sayar da man a farashi daya da MRS ba, domin matatar Dangote ba ta kai mana fetur kai tsaye kamar yadda aka tsara ba.
“Muna karbar man ne ta hannun MRS, sannan mu kara kashe kudi wajen kai shi gidajen mai namu, don haka ba za mu iya gogayya da MRS ba, wadda ita ce mai samar mana,” in ji shi.
