Sabunta Manhajoji: Gwamnatin Tarayya Ta Ware N580m a Filayen Jiragen Sama

Gwamnatin Tarayya ta ware kuɗaɗen Naira miliyan 580 domin sayo na’urorin sanyaya iska (chillers) da kuma sabunta manhajojin kwamfuta a wasu filayen jiragen sama a ƙasar nan. Wannan na daga cikin jimillar kasafin kuɗi na Naira biliyan 87.3 da aka tanada wa ɓangaren sufurin jiragen sama a cikin kudirin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Takardar kasafin kuɗin ba ta fayyace takamaiman irin manhajojin da za a sabunta ba, sai dai ta nuna cewa an ware Naira miliyan 500 domin sayo chillers na Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, yayin da aka ware Naira miliyan 80 domin sabunta tsarin kula da harkokin kuɗi da wasu manhajoji.

Baya ga sayo chillers da sabunta manhajoji, gwamnatin na shirin samarwa ko inganta ayyukan Wi-Fi ga fasinjoji a filayen jiragen sama biyar na ƙasa da ƙasa da kuma wasu na cikin gida, a kan kuɗin Naira miliyan 800. Haka kuma, za a girka na’urorin sanyaya ruwa (water-cooling chillers) a filayen jiragen sama na Legas da Abuja, a kan kuɗin Naira miliyan 500.

A cewar takardar kasafin, gwamnatin za ta kuma gina cibiyar sarrafa najasa (sewage treatment plant) a Filin Jirgin Sama na Owerri a kan kuɗin Naira miliyan 21, tare da shirya taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyoyin ma’aikatan sufurin jiragen sama sau biyu a shekara, a kan kuɗin Naira miliyan 150.

Dangane da ayyukan gyaran da aka shirya aiwatarwa a shekarar, takardar ta bayyana cewa za a rufe tsage-tsage a titinan sauka da tashi na jirage (runways), filayen ajiye jirage (aprons) da hanyoyin zirga-zirgar jirage (taxiways) a manyan filayen jiragen sama na Port Harcourt, Kano da Legas, a kan kuɗin Naira miliyan 800. Haka kuma, za a sayo tare da girka tsarin hasken filin jirgi (airfield lighting systems) a Filin Jirgin Sama na Ilorin, a kan kuɗin Naira miliyan 800.

Takardar kasafin kuɗin ta nuna cewa an ware Naira 14,779,174,252 domin biyan albashin ma’aikata, Naira 2,338,000,548 domin kuɗaɗen gudanarwa (overhead), yayin da aka tanadi Naira 70,192,789,683 domin manyan ayyuka (capital projects) a ma’aikatar.

Har ila yau, an nuna cewa an ware Naira 33,906,953,400 domin gyarawa da inganta kayayyakin more rayuwa a filayen jiragen sama, ciki har da gine-ginen tashoshi, titinan jirage, filayen ajiye jirage da shinge, a cikin shekarar.

Manyan abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a kasafin ma’aikatar sun shafi manyan ayyukan gine-gine da inganta kayayyakin more rayuwa. Takardar ba ta ƙunshi tanadin kuɗaɗen shiga na kai tsaye (retained independent revenue) ko tallafi da gudummawar ƙasashen waje ba.

Kudirin kasafin ya nuna cewa Naira biliyan 70.19, wato sama da kashi 80 cikin 100 na jimillar kuɗin da aka ware, an tanade su ne domin manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira biliyan 14.78 domin albashin ma’aikata da Naira biliyan 2.34 domin kuɗaɗen gudanarwa.