Yarjejeniyar Najeriya da UAE Zai Soke Haraji kan Kayayyaki 7,315

Gwamnatin Tarayya ta kulla Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki (Comprehensive Economic Partnership Agreement – CEPA) da Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), domin soke haraji kan dubban kayayyaki.

Wani mamba a Hukumar Gudanarwa ta Hukumar Raya Arewa Maso Gabas (NEDC), Hon. Sam Onuigbo, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, ranar Talata. Ya ce muhimmin abin da ya faru a Abu Dhabi shi ne yarjejeniyar CEPA da Najeriya ta rattaba hannu da UAE a yayin Taron Makon Dorewar Ci gaba na Abu Dhabi, wanda aka gudanar daga ranar 11 zuwa 15 ga Janairu.

NAN ta ruwaito cewa Onuigbo tsohon dan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia ta Arewa da Kudu, kuma ya taba zama Shugaban Kwamitin Sauyin Yanayi na Majalisar Wakilai a Majalisa ta 8.

Ya ce, “An rattaba hannu kan yarjejeniyar CEPA a watan Janairun 2026, kuma UAE za ta soke haraji kan kayayyaki 7,315 daga Najeriya. Daga ciki, kayayyaki 2,805, wato kashi 38.3 cikin 100, za su samu damar shiga ba tare da biyan haraji nan take ba, yayin da sauran za a soke harajin a kansu cikin shekaru uku zuwa biyar. Wannan ya shafi kayayyakin noma da na masana’antu.

“Haka nan, a ƙarƙashin yarjejeniyar CEPA tsakanin Najeriya da UAE, wadda ita ma aka sanya hannu a kanta a Janairun 2026, Najeriya ta soke haraji kan kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga UAE. Wannan yarjejeniya na ƙirƙirar manyan damar kasuwanci tsakanin ’yan Najeriya da Ƙasar Emirates,” in ji shi.

Onuigbo ya ce yarjejeniyar babbar nasara ce, wadda za ta sauƙaƙa wa ’yan kasuwa a Najeriya — musamman masu kasuwanci masu rijista da sahihanci — damar zuwa UAE domin buɗe ofisoshi, yin aiki na tsawon watanni uku, sannan su koma gida.

Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan rattaba hannu kan yarjejeniyar, yana mai cewa an tsara ta ne domin sake farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya, samar da yanayi mai kyau ga zuba jari da ayyukan yi, tare da inganta jin daɗin jama’a.

Ya ƙara da cewa, “Najeriya a shirye take don kasuwanci. Haka kuma, an ƙaddamar da Tsarin Manufofin Kasuwar Carbon ta Najeriya a Abu Dhabi.”
Onuigbo ya bayyana cewa Najeriya, wadda ke da yawan jama’a kusan miliyan 250, ta dade tana fuskantar matsalar ƙarancin wutar lantarki da makamashi, lamarin da ke hana ta cimma manufofinta na tattalin arziki da masana’antu.

Ya ce, “Saboda haka, Najeriya ta ɗauki matakai da dama, ciki har da Tsarin Canjin Makamashi (Energy Transition Plan), dokar Sauyin Yanayi, da Dokar Wutar Lantarki, wadda Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu a kanta kwanaki takwas kacal bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

“Wannan na nuna muhimmancin magance gibin makamashi, domin samun isasshen wutar lantarki muhimmin ginshiƙi ne wajen bunƙasa masana’antu da ci gaban ƙasa.”
Onuigbo ya yaba da rawar da Najeriya ta taka a taron Abu Dhabi, yana mai cewa taron zai ƙara buɗe ƙofofin damar tattalin arziki a duniya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da UAE.

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar da Shugaban Ƙasa ke jagoranta za ta taimaka wajen magance ƙalubale da mummunan tasirin sauyin yanayi, tare da ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2026.
— NAN