2027: Takardar Atiku Na Iya Kawo Rabawa a ADC — Baba-Ahmed

Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi gargadin cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na iya fuskantar rarrabuwar kai a cikinta idan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar gabanin zaben 2027.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya yi nazari kan barazanar rikice-rikice da ke kunno kai a cikin jam’iyyar adawa da ke samun goyon bayan wata kawance.

A cewarsa, Atiku na da karfin da zai ba shi damar lashe tikitin takarar ADC da zarar jam’iyyar ta gudanar da babban taronta na kasa, amma hakan na iya jawo ficewar wasu ‘yan jam’iyyar masu burin takarar shugaban kasa.

“Idan ADC ta je babban taro — kuma za ta je, domin wannan shi ne abin da Atiku ke so — akwai yiyuwar shi ne zai samu tikitin,” in ji Baba-Ahmed.

“Idan hakan ta faru, mutane da dama za su fice, domin da yawa daga cikin wadanda ke cikin jam’iyyar a yanzu suna can ne da buri daya: su zama shugaban kasa.”

Ya bayyana cewa ADC a halin yanzu na dauke da manyan ‘yan siyasa masu karfi da buruka masu kama da juna, wanda a cewarsa hakan ba makawa zai haifar da rikici da zarar aka fara fafatawa kan tikitin takara.

Baba-Ahmed ya kuma yi tsokaci kan rawar da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ke takawa, yana mai cewa salon siyasar Obi bai dace da yanayin zaben fidda gwani mai cike da fafatawa ba.

“Peter Obi kamar yana cewa ne, ‘Ban zo neman matsayi na biyu ko siyasar babban taro ba. Na zo ne domin in rike tutar jam’iyyar,’” in ji shi.

A cewarsa, Obi a tarihi ya kan fito ne ta hanyar yarjejeniyar fahimta (consensus), ba ta hanyar fafatawa mai tsanani ba, wanda ya ce hakan na iya zama da wahala a cikin ADC.

“Ba kasafai yake shiga babban taro ba. Yakan zo ne domin a amince da shi,” Baba-Ahmed ya kara da cewa, yana mai gargadin cewa irin wannan tsammani na iya kara dagula al’amura yayin da sauran ‘yan takara ke neman damar fafatawa daidai.

Ya kammala da cewa babban taron ADC na iya zama juyin juya hali ga jam’iyyar. “Jam’iyyar za ta zubar da jini bayan taronta. Kusan tabbas Atiku zai lashe tikitin, kuma idan hakan ta faru, wasu mutane za su fice,” in ji Baba-Ahmed.