Safarin Kayayyakin da ba Man Fetur Sun Kai Dala Biliyan 6.1 a 2025 – NEPC

Bangaren fitar da kayayyakin da ba man fetur ba a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba a shekarar 2025, inda ya kai jimillar kudin da ya kai dala biliyan 6.1.

Wannan ya nuna karin kashi 11.5 cikin 100 idan aka kwatanta da dala biliyan 5.4 da aka samu a shekarar 2024, lamarin da ke nuni da ci gaba da Najeriya ke samu wajen rage dogaro da man fetur tare da bunkasa sauran sassan tattalin arziki.

Babban Darakta kuma Shugabar Hukumar Inganta Fitar da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC), Nonye Ayeni, ce ta bayyana hakan yayin gabatar da rahoton ci gaban shekara da hasashen fitar da kayayyaki na 2026 a Abuja, ranar Litinin.

Ta ce wannan nasara ta samo asali ne daga karuwar yawan kayayyakin da ake fitarwa da kuma fadada kasuwannin da kayayyakin Najeriya ke shiga, wanda ke nuna karuwar shigar kasar cikin kasuwannin duniya.

Bayanan da hukumomin duba kaya kafin fitarwa suka tattara, kamar yadda NEPC ta ambata, sun tabbatar da cewa bangaren fitar da kayayyakin da ba man fetur ba ya kafa sabon tarihi.

“In bangaren fitar da kayayyakin da ba man fetur ba, an samu kusan dala biliyan 6.1, wanda ke wakiltar karin kashi 11.5 cikin 100 idan aka kwatanta da dala biliyan 5.4 da aka samu a 2024,” in ji Ayeni.

Ta kara da cewa wannan shi ne mafi girman darajar da aka taba samu a fitar da kayayyakin da ba man fetur ba ta hanyar hukuma tun bayan kafa NEPC kusan shekaru 50 da suka wuce, inda ya zarce dukkan tarihin da aka taba samu a baya.

Shugabar NEPC ta kuma bayyana cewa karin ya shafi yawan kayayyakin da aka fitar, inda jimillar fitar da kayayyakin da ba man fetur ba ta kai miliyan 8.02 na tan metrik a shekarar 2025, idan aka kwatanta da miliyan 7.29 na tan metrik a 2024, wanda ke nuna karin kashi 10 cikin 100.