Karancin Albashi: NLC ta bukaci a Biya Ma’aikatan Jihar Lagos Naira 150,000

Kungiyar kwadago na kasa

Sashen jihar Legas na kungiyar kwadago ta ƙasa, Nigeria Labour Congress (NLC), ya bukaci sabon mafi ƙarancin albashi na ₦150,000 ga ma’aikatan jihar, bisa la’akari da tashin farashin rayuwa da kuma karin albashin da aka yi a jihohin Imo da Ebonyi.

Shugabar NLC ta jihar Legas, Funmi Sesi, ce ta yi wannan kira a ranar Alhamis, tana mayar da martani kan karin albashin da gwamnoni biyu suka aiwatar a jihohinsu.

Ta ce a halin yanzu ma’aikatan Legas na karɓar mafi ƙarancin albashi na ₦85,000, wanda ya kamata a duba a ƙara shi saboda tsadar haya, sufuri, abinci da kuma wutar lantarki a Legas.

“Lokaci ya yi da za a duba a ƙara mafi ƙarancin albashi a Legas. Aƙalla wani ya fara ɗaukar mataki, kuma ya buɗe hanyar da sauran za su bi,” in ji ta.

Sesi ta ƙara da cewa babu wanda zai iya zargin Gwamna Babajide Sanwo-Olu idan ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi, domin ma’aikatan jihar sun cancanci samun kyakkyawan albashi da yanayin aiki mai kyau, da ya dace da halin tattalin arziki musamman a Legas.

Shugabar ta bayyana kwarin guiwa cewa dukkan gwamnatocin jihohi za su bi sahun Imo da Ebonyi.

A baya-bayan nan ne Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashi daga ₦76,000 zuwa ₦104,000 ga ma’aikatan jihar.

Haka zalika, gwamnatin jihar Ebonyi ta daga mafi ƙarancin albashi daga ₦70,000 zuwa ₦90,000.